Na Damu da Yadda Majalisar Dokokin Najeriya ke Tafiyar da Batun Ciyo Basussuka da Gwamnatin Tarayya ke yi – Sanata Ndume

 

Sanata Ali Ndume ya nuna damuwarsa kan yadda gwamnatin tarayya ke karbo bashi a cikin matsanancin halin tattalin arzikin da ke fuskantar kasar.

Ndume bai ji dadin yadda majalisar kasa ta gaggauta mayar da martani kan rokon da shugaba Buhari ya yi na karbo basussuka ba.

A halin da ake ciki, martabar bashin Najeriya na ci gaba da karuwa yayin da shugaban kasa ya gabatar da wani sabon bukatar ranto kudi a gaban majalisar dattijai.

FCT, Abuja – Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji, Sanata Ali Ndume, ya ce ya damu da yadda majalisar dokokin Najeriya ke tafiyar da batun ciyo basussuka da rance da gwamnatin tarayya ke yi.

Channels TV ta rawaito cewa Ndume yayi wannan furuci ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba, inda ya nuna matukar damuwa game da yadda majalisar kasa ta dauki bukatar ciyo bashin na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A watan Yuli ne Majalisar Dattawa ta amince da shirin karbo bashin gwamnatin tarayya na shekarar 2018-2020 na dala biliyan 8.3 da Yuro miliyan 490.

Jaridar Premium Times ta kuma rawaito cewa Ndume abun da ya kuma fi damun shi shine cewa babu abin nunawa wanda za a ce an yi da kudin da aka ranto.

Ya kuma ce ya kamata a zauna sosai ayi nazari sannan a nemi sanin ra’ayin mutanen da ake wakilta ba wai kawai majalisa ta zauna tace ta amince da ciyo bashin ba.

Ndume ya ce:

“Ciyo bashi ba laifi bane amma lokacin da adadin bashin ya ƙaru wanda na fahimci yana kusa da kashi 80 zuwa 90 cikin ɗari, dole ne mutum ya yi taka tsantsan.

“Abin da ke damuna kuma shine yadda Majalisar Dattawa ke bi da lamarin. Majalisar dattijai a ma’anarsa gidan ne na shawara a lokacin da abubuwa irin wannan suka zo, ba kawai mu hanzarta mu ce saboda ana yi maka kallon mutum nagari sai kayi hanzarin amincewa da shi ba” .

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here