‘Yan Ta’addan Boko Haram Sun Sace Taraktoci 5 Tare da Kona 2 a Jahar Yobe

 

Wasu miyagu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun sace tarakta biyar tare da kurmushe biyu.

An gano cewa ‘yan ta’addan sun shiga kauyen Ngelbuwa da ke karamar hukumar Gujba ta jahar Yobe.

Sun bi sako da lunguna inda suka san akwai tarakta tare da kai wa direbobin farmaki kuma suka kwace.

Gujba, Yobe – Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun yi awon gaba da tarakta biyar tare da kone wasu biyu a Ngelbuwa da ke karamar hukumar Gujba ta jahar Yobe.

Daily Trust ta rawaito cewa, wani mazaunin garin mai suna Kyari Konto, ya ce ‘yan ta’addan sun kutsa garin inda suka dauka wani mazaunin garin wanda suka umarcesa da ya nuna musu gidajen da manoma ke da tarakta.

Shugaban wata kungiyar arewa maso gabas, reshen jahar Yobe, Nuhu Baba Hassan, ya bayyana cewa an sace taraktoci uku da suke mallakin kungiyar reshen jahar Borno da Yobe.

Ya ce taraktan da ke karkashin ikonsa duk an kwace daga hannun matukin yayin da aka nuna masa bindiga.

Shugaban ofishin ‘yan sandan yankin Buni Yadi, Bitrus Mamuda Saleh, ya tabbatar da aukuwar lamarin, Daily Trust ta rawaito hakan.

Ya ce Muhammad Mustafa, shugaban NECAS reshen jahar Borno, ya ruwaito yadda ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai wa direbobin tarakta na kauyen Ngelbuwa da ke Gujba kuma suka sace tarakta hudu mallakin gwamnatin jahar Borno.

Ya ce ‘yan ta’addan sun kara da banka wa taraktocin NECAS biyu wuta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here