Majalisar Dokokin Jihar Kano ta Dakatar da Shugaban ƙaramar Hukumar Gwale, Khalid Diso

 

Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da Ciyaman ɗin karamar hukumar Gwale, Khalid Ishaq Diso, bisa zargin sayar da kadarorin gwamnati.

Shugaban majalisa, Yusuf Isma’il Falgore, ya ce wasu daga cikin Kansilolin yankin ne suka shigar da ƙorafi kan Ciyaman.

A halin yanzu majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi da zai gudanar da bincike kana ta umarci mataimakin ciyaman ya maye gurbin na tsawon wata 3.

Jihar Kano – Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Honorabul Khalid Ishaq Diso, na tsawon watanni uku.

Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne yayin da ta amince da rahoton kwamitin kula da harkokin kananan hukumomi da naɗe-naɗen sarauta a zamanta na ranar Talata.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa majalisar ta yi haka ne bayan an kawo mata ƙorafin cewa shugaban ƙaramar hukumar na sayar da kadarorin gwamnati ba bisa ka’ida ba.

A cewar majalisar, shida daga cikin Kansilolin ƙaramar hukumar Gwale, da mambobi 10 ne suka shigar da ƙorafin abin da Ciyaman ɗin yake aikata wa.

A jawabin shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Honorabul Yusuf Isma’il Falgore, ya ce ana zargin ciyaman ɗin da yanke hukunci bisa ra’ayin kansa ba tare da tuntuɓar kansiloli ba.

Yadda majalisar Kano ta bi matakan bincike Bayan samun waɗan nan ƙorafe-ƙorafe kan Ciyaman ɗin, majalisar dokokin Kano ta kafa kwamitin wucin gadi, wanda ta ɗora wa alhakin gudanar da bincike don tabbatar da zargin.

Ta kuma bai wa kwamitin wa’adin kwanaki 60 watau tsawon watanni biyu ya kammala bincike kuma ya kawo mata rahoton abubuwan da ya gano.

Daga nan sai majalisar ta umarci mataimakin shugaban ƙaramar hukumar ya karɓi ragamar harkokin mulkin Gwale na tsawon watanni 3 gabanin kammala bincike, rahoton Nigerian News.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com