Majalisar Kansiloli ta Cire Shugaban Karamar Hukumar Shiroro

Majalisar Kansiloli ta tsige Shugaban Ƙaramar Hukumar Shiroro, Kwamred Dauda Suleiman Chukuba, bisa zargin Almundahana.

A cewar majalisar, sun bawa shugaban duk wata dama domin ya kawar kansa daga zargin da ake yi masa amma sai ya nuna musu raini.

Ana zargin Kwamred Chukuba da yin almubazzaranci da barnatar da kudaden shiga da karamar hukuma ta samu.

Kwamred Suleiman Dauda Chukuba, shine tuɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Shiroro da aka sauke daga kan kujerarsa.

An tsige shi bisa zargin cire kuɗaɗe tare da murƙushe harajin ƙaramar hukuma ba tare da samun sahalewa daga ƴan majalisar su ba, kamar yadda Vanguard ta rawaito ranar Talata.

Sannan kuma ya yi almubazzaranci da kuɗaɗe.

Mambobi goma sha ɗaya daga cikin Kansiloli goma sha huɗu sun kaɗa kuri’ar tsige shugaban ƙaramar hukumar.

Wasu ƙarin zarge-zarge da ake yiwa Shugaban ƙaramar hukumar sun haɗar da kashe kuɗaɗen harajin ƙaramar hukuma ba tare da samun sahalewar majalisar Kansiloli ba, almubazzaranci da sauransu.

Sauran sun haɗar da laifukan almundahanar kuɗaɗe, ƙin gurfana gaban majalisa na tsawon shekara guda don bayanin ƙiyasin haraji da adadin kuɗaɗen da ƙaramar hukuma ta samu.

Sun ƙara zargin cewa bayan samun sahalewar cire ₦7,000000 daga asusun ƙaramar hukuma don shiryawa musu taron sanin makamar aikin bita, an shafe tsawon watanni huɗu, amma har yanzu bulumbuƙwui, babu wani labari ko batu kan kuɗaɗen.

Shugaban ƴan majalisa, Malam Yusuf Aliyu, shine ya jagoranci zaman tare da mambobin majalisar 14.

Ƴan majalisar su 14 sun nufi gidan gwamnati dake Minna bayan zartar da hukuncin don shawara da wasu ƙusoshin gwamnati akan batun.

An kasa samun tuɓaɓɓen ƙaramar hukumar don maida martanin kare kansa daga zarge-zarge da ake yi masa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here