Majalisar Dokokin Jihar Legas ta yi Fatali da Sunayen Mutane 17 da Gwamna Sanwo-Olu Yake so su Zama Kwamishinoni
An tantance wadanda Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bada sunayensu domin zama Kwamishinoni.
‘Yan majalisar dokokin Legas sun amince da mutane 22 ne, amma mutane fiye da 15 ba su samu shiga ba.
Zuwa yanzu ba a ji dalilin kin yarda da ragowar ba, majalisar ba za ta sake zama ba sai a makon gobe.
Lagos – Majalisar dokokin jihar Legas ta yi fatali da wasu daga cikin mutanen da Gwamna Babajide Sanwo-Olu yake so su zama kwamishinoni.
The Cable ta kawo rahoto cewa a jerin mutane 39 da Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya ba majalisa sunayensu, 22 ne kadai aka yi amincewa da su.
Tun kafin a ki karbar ragowar mutane 17 da aka bada, wasu su ka rika yin korafi, ana zargin gwamnatin Legas da rashin adalci a rabon mukaman.
Kwamishinonin da aka tantance:
1. Misis Folashade Adefisayo
2. Farfesa. Akin Abayomi
3. Mista Yomi Oluyomi
4. Misis Folashade Ambrose
5. Miss Barakat Bakare
6. Mista Gbenga Omotosho
7. Injiniya Olalere Odusote
8. Dr. Rotimi Fashola
9. Misis Bolaji Cecilia Dada
10. Mista Sam Egube
11. Mista Olalekan Fatodu
12. Misis Solape Hammond
13. Mista Mosopefolu George
14. Injiniya Aramide Adeyoye
15. Mista Seun Osiyemi
16.Mr Rotimi Ogunwuyi
17. Dr. Olumide Oluyinka
Read Also:
Hon. Mudashiru Obasa ya jagoranci Majalisa
Rahoton da Vanguard ta fitar a yammacin Laraba ya ce Rt. Hon. Mudashiru Obasa ya jagoranci zaman majalisar dokokin da aka yi a garin Ikeja.
A cewar Mudashiru Obasa, kwamitin da ya yi wannan aiki ya bi tsauraran matakai wajen tantance wadanda za su rike kujerar kwamishononin.
Shugaban majalisar ya ce shugaban masu tsawatarwa, Hon. Fatai Mojeed mai wakiltar Ibeju-Lekki tun a 2015 yake jagorantar kwamitin.
Kwamishononin da aka amince:
1. Layode Ibrahim
2. Mista Mobolaji Ogunlende
3. Dr. Dolapo Fasawe
4. Bola Olumegbon
5. Mista Idris Aregbe
6. Miss Abisola Ruth Olusanya
7. Mista Moruf Akinderu Fatai
8. Mista Kayode Bolaji-Roberts
9. Injiniya Abiola Olowu
10. Misis Toke Benson-Awoyinka
11. Dr. Oreoluwa Finnih- Awokoya
12. Mista Yakub Adedayo Alebiosu
13. Mista Lawal Pedro SAN
14. Mista Tunbosun Alake
15. Mista Gbenga Oyerinde
16. Dr. Adekunle Olayinka
17. Dr. Jide Babatunde
18. Mista Afolabi Ayantayo
19. Mista Tokunbo Wahab
20. Mista Olakunle Otimi-Akodu
21. Mista Jamiu Alli-Balogun
22. Mista Abdulkabir Ogungbo
Game da wadanda aka amince a rantsar da su, majalisar dokokin ta tuna masu gwamnatin Legas da mutanen su ka zo yi wa aiki ba daidaiku ba.
Rahoto ya ce sai ranar 28 ga Agustan nan ‘yan majalisar dokokin jihar za su sake zama