Gabannin Zanga-Zanga: Majalisar Wakilan Najeriya na Ganawa da Matasa a Abuja

 

Majalisar wakilan Najeriya ta fara zaman gaggawan da ta tsara yi yau, Laraba domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ƙasar.

A farkon makon nan ne, majalisar ta sanar da katse hutunta na shekara da ta soma ranar 23 ga watan Yulin 2023 domin yin zaman.

Zaman na zuwa ne sa’oi kafin soma zanga-zangar da wasu ƴan Najeriya ke shirin yi domin nuna damuwa game da matsi da tsadar rayuwa da ake ciki a ƙasar.

A zaman na yau, majalisar ta gana da ƙungiyoyin matasa domin sauraron buƙatunsu da nufin miƙa su ga shugaba Bola Tinubu.

Ɗan majalisa mai wakiltar jihar Kaduna ta arewa a majalisar wakilai, Muhammad Bello El Rufai ya shaida wa BBC cewa ganawa da matasa na da muhimmanci domin majalisar ta san abubuwan da ke damun su.

Ya ce duk da kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da damar yin zanga-zanga, amma “ba ma so a samu tashin hankali kamar yadda muka gani a wasu ƙasashen – Kenya da Sudan.”

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa hakan bai zama dalili na hana mutane bayyana ra’ayoyinsu tare da nuna damuwarsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here