Majalisar Wakilai ta Koka da Rashin Tsaro

 

Mambobin kungiyar marasa rinjaye a majalisar wakilai sun koka kan halin da kasar ke ciki na rashin tsaro.

Sun kuma bayyana cewa ‘yan Najeriya basu cancanci shiga wannan mawuyacin yanayi da suke ciki ba.

A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar, sun nemi a yi bincike kan harin da ‘yan bindiga suka kai NDA.

Abuja – Mambobin kungiyar marasa rinjaye a majalisar wakilai sun bayyana cewa ‘yan Najeriya ba su cancanci halin da suke ciki ba wanda ya zama ruwan dare a baya-bayan nan.

Koken nasu wanda ke kunshe a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai, Ndudi Elumelu, yana magana ne a kan karuwar ayyukan ta’addanci da hare -haren ‘yan bindiga a cikin kasar.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“’Yan Najeriya ba su cancanci shiga cikin wannan mummunan yanayin ba.”

‘Yan majalisar sun kuma bukaci jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke jagorantar gwamnatin da ta dauki tsauraran matakai don ceto ‘yan Najeriya daga rashin tsaro, Channels TV ta rawaito.

Mambobin hamayyar a zauren majalisar sun ci gaba da cewa sun firgita, musamman kan mamayar da aka kaiwa Kwalejin horar da sojojin Najeriya (NDA) wanda ya haifar da kisa da sace wasu jami’an sojoji.

Sun koka kan yadda ake kai hare-hare sansanonin sojoji da kuma kisan ganganci da ‘yan bindiga ke yiwa ‘yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba duk da tabbacin da ake samu daga gwamnati mai ci.

Bayan dogon nazari, ‘yan majalisar sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa don magance mummunan halin da ake ciki da kuma ceto kasar daga durkushewa.

Sun kuma nemi a gaggauta gudanar da bincike kan yanayin da ya ba da damar mamaye NDA da kashe -kashe da sace jami’an, Vanguard ta rawaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here