Gwamnonin APC Sun Yaba da Jagorancin Gwamna Zulum

 

Kungiyar gwamnonin APC ta aike ta sakon taya murnar ranar haihuwa ga gwamna Babagana Umaru Zulum.

Gwamnonin sun bayyana cewa Zulum na taka muhimmiyar rawa wajen yaki da matsalar tsaro a faɗin Najeriya.

A ranar 26 ga watan Agusta, 2021, Gwamnan Zulum ya cika shekara 52 a duniya.

Borno – Kungiyar gwamnonin APC (PGF), ranar Alhamis ta jinjinawa gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, bisa abinda ta kira kyakkyawan jagoranci da yake gudanarwa, kamar yadda punch ta rawaito.

Wannan na kunshe a cikin wani sako mai taken, “Sakon taya murnar ranar haihuwa ga mai girma Farfesa Babagana Umaru Zulum.”

Sakon na ɗauke da sa hannun shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jahar Kebbi, Atiku Bagudu, wanda aka fitar a Abuja.

Kungiyar PGF ta kunshi dukkan gwamnonin da aka zaɓa karkashin inuwar jam’iyyar APC a faɗin kasar nan.

Muna tayaka murna da dukkan iyalanka

Wani sashin sakon gwamnonin yace:

“Muna taya mai girma gwamna murnan zagayowar wannan rana mai muhimmanci, iyalanka da kuma al’ummar jahar Borno baki ɗaya.”

“Muna jinjina gare ka bisa jagorancinka wanda ya kasance abin koyi, kyawawan kudirorinka da kokarinka na haɗa kai da kawo zaman lafiya a Najeriya.”

“Karkashin jagorancin jam’iyyar mu APC, da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kana taka muhimmiyar rawa wajen yaki da Boko Haram a arewa maso gabar da matsalar tsaro a sassan Najeriya.”

Zamu cigaba da aiki tare domin kawo cigaba

Gwamnonin sun bayyana cewa suna taya mai girma gwamna, Farfesa Babagana Umaru Zulum murnar wannan rana.

Hakanan kuma gwamnonin sun jaddada cewa a shirye suke a ɗora daga inda aka tsaya wajen haɗa karfi-da-karfe tare da gwamnatin tarayya karkashin shugaba Buhari, a aiwatar da shirye-shiryen da zasu amfani al’umma.

A cewar gwamnonin zasu cigaba da aiki tare domin samar da ayyukan yi, yaki da matsalar tsaro, farfado da tattalin arziki da kuma kawar da talauci tsakanin yan Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here