Yakubu Gowon: Majalisar Wakilai ta yi Martani Akan Dan Majalisar Birtaniya
Majalisar dattawa ta kira wani babban dan majalisar Birtaniya.
Dan majalisar ya yi suka ga tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon.
A ranar 23 ga watan Nuwamba, Tugendhat ya yi wa Gowon kazafin sata.
Majalisar dattawa ta kira wani babban kwamishinan Birtaniya zuwa Najeriya a kan wani tsokaci da wani dan majalisar Birtaniya, Tom Tugendhat yayi a kan tsohon shugaban kasan Najeriya, Yakubu Gowon, Thisday ta wallafa.
Read Also:
A ranar 23 ga watan Nuwamba, ana tsaka da wata muhawara a kan majalisar UK na korafin da ‘yan Najeriya suka yi a kan hukunta jami’an tsaron da suke da hannu a kan kashe-kashen Lekki Toll Gate, ya zargi Gowon da kwashe rabin kudin CBN ya gudu dasu lokacin da ya bace.
A cewarsa: “Akwai mutanen da za su tuna lokacin da Janar Gowon ya bar Najeriya da rabin kudin CBN, kuma ya tare a Landan.”
Amma bayan komawarsu majalisar ranar Talata, Tugendhat ya bukaci majalisar ta bayar da hakuri ga Gowon da sauran ‘yan Najeriya.
Majalisar wakilai ta tilasta kwamitinta na harkokin kasashen ketare da ta shiga ta tattauna da kwamitin harkokin kasar waje na majalisar Birtaniya a kan wannan tsokacin.
Hon Yusuf Gagdi ya ce wannan kazafin da dan majalisar Birtaniya yayi ba shi da tushe balle makama. Sannan ya ce wannan kazafin zai iya kawo tashin hankali da rikici, wanda zai iya janyo cece-kuce a kasa.