Shugaban Kasa: Majalisar Wakilai ta yi Martani Kan Dokar Majalisar
Majalisar wakilai na neman gabatar da wani kudiri da zai tursasa zababben shugaban kasa ko gwamna bayyana yan majalisarsa cikin kwanaki 30 bayan karban mulki.
Sabuwar dokar na kuma neman majalisa ta tsige duk shugaban kasa ko gwamnan da ya gaza aikata hakan ba tare da kwakwaran dalili ba.
Mista Kpam Sokpo ne ya gabatar da wannan batu a zauren majalisar a ranar Laraba.
Majalisar wakilai na neman sabon shugaban kasa ko gwamna ya kafa majalisarsa cikin kwanaki 30 bayan rantsar da shi ko ya fuskanci barazanar tsigewa daga majalisar dokokin tarayya ko na jiha, jaridar Punch ta ruwaito.
Read Also:
Dokar mika mulki da hawa kujerar mulki, 2020, Mista Kpam Sokpo ne ya gabatar da ita inda a cikinta ne wannan bukata yake, ya kuma gabatar da shi a majalisa ne a ranar Laraba.
Dokar ta kuma nemi a samar da kudade na musamman ga kwamitin mika mulki da kuma tursasa gwamnonin jiha sanar da yan majalisunsu a cikin wannan lokaci.
Ya zo kamar haka:
“Bisa ga sassa na 147 da 302 na kundin tsarin mulki, da zaran shugaban kasa ya kama aiki, zai nada ministoci cikin kwanaki 30 daga ranar da ya karbi rantsuwar kama aiki.
“Shugaban kasar zai kafa tare da nada dukkanin gwamnatocin hukumomi da masana’antun da suka isa ayi nade nade cikin watanni biyu daga ranar da ya karbi mulki.
“A inda Shugaban kasar ya gaza ba dokokin hadin kai ba tare da kwakwaran dalili ba, toh za a kama shi da laifin saba ka’ida kamar yadda yake a karkashin sashi na 143(2) na kundin tsarin mulki.”