Idan Malamai Basu Fadawa Shugabanni Gaskiya a Munbari ba, a Ina Zasu Fada ?
Ita gaskiya, gaskiya ce indai gaskiyar ce.
Yayin da aka tozarta gaskiya, ko kuma sai an zabi wanda za’a gayawa gaskiya ma’ana sai masu rauni (Talakawa) za’a gayawa gaskiya babu shakka an tozartadda gaskiya.
Mecece gaskiya kuma a ina za’a fadi Gaskiya?
A takaice Gaskiya, Nasiha ce, wadda ake fadawa mutum/mutane cikin zance ko a wa’azance kamar yadda Malamai keyi idan zasu warware Zare-da-abawa kan wani abu yayin da suke kan munbarin khudba da ma a kowanne zarafi da suka samu na fede gaskiya.
Irin wannnan muhimmin aiki na fadar gaskiya, ana iya yinsa a ko ina matukar akwai zarafin yin hakan. Kuma gaskiya ta kowa ce. Ma’ana ana iya gayawa kowa gaskiya tunda dai kamar yadda nace a takaice gaskiya Nasiha ce, Ana iya yiwa Shugabanni/Masu mulki masu kudi da Malam Talaka.
Me ye aibu idan an fadi gaskiya?
Matukar gaskya gaskiyar ce babu wani aibu ga dukkannin bangarori biyu wato ga wanda ya fadi gaskiya da kuma wanda aka fadawa gaskiyar, Amma kuma ita gaskiya daci gare ta. Domin ina iya tunawa yadda a wake, Marigari Sa’adu Zungur ke fadi.
Muddun mutum ko mai wa’azi akan gaskiya yake magana, to kuwa komai fadin gaskiyar ya jawo ta biya, cewar Sa’adu Zungur cikin wakensa.
Yadda malamai a dukkannin sassa suka dada zage damara wajen tunasar da Shugabanni halin da kasa ke ciki na rashin tsaro da kuncin rayuwa da ake ciki a yanzu abin a yaba ne, domin duk Dan’Adam kasasshe ne a koda yaushe yana bukatar a tunasar dashi game da yin abinda ya kamata, kuma ina kyautatawa Malaman nan zaton cewa sunayi ne domin neman gyara.
Ace a wayi gari ana yiwa malamai barazarar rabasu da wurare ko munbarorin wa’azinsu domin kawai suna isar da nasiha ga shugabanni kai tsaye daga inda suke da ikon aikewa da sako/wa’azi, yin hakan tamkar komawa zamanin jahiliyya ne.
Masu cewa, Malamai ba za su yiwa shugabanni Nasiha ko jan hankalinsu akan munbarin karatu/Khudba ba, To a ina kuke so suyi ?
Shin kuna zaton duk wanda nasiha batayi masa dadi gada munbari ba zayi yi masa dadin ji idan gaka-ga-shi a fadarsa?
Shin ko kuma kuna ganin cewa su wadanda ke kewaye da shugabanni da kuma Yan sakai wato yan jagaliyar dake kewaye da shugabannin zasu bar Malami ya samu ganin shi (shugaban) cikin karamci, domin ni dai a iya sani na a halin da ake ciki ganin shugabanni musamman na Siyasa ba sauki bare shi ba a irin wannan yanayi da Yan bani na iya ke kewaye da fadar masu mulki domin kwadayin wani abu.
Haka kuma ina kuka kai tunanin da mafi yawan mutane suke yi cewa, akasarin wadan da shugabanni ke rufe kofa dasu, sunje karbar nasu kason ne musamman idan akaga Malami ne ?
A tambayi duk wani shugaba cewa ya yake ji idan akace gashi can Malam wane akan munbarin karatu/khudbar sa ya na fahimtar da jama’a game da wani abin alkhairi da shugaban yayi ko kuma ma ace gashi can yanayi masa addu’a tare da Dalibansa ?
Idan har yin hakan ba ketare hakkin iyakar malunta bane, To ta yaya yin wa’azi gare shi akan ya gyara wani abu da yake damun Jama’a akan munbarin da ada aka yabeshi zai zama kuskure? Kuma idan har yabon da Malamai kewa shugabanni akan munbari yayin da sukayi abin yabo bai zama siyasa ba ta yaya gaya musu cewa su gyara ya zama siyasa ?
Read Also:
Dogaro da wannan nazari nake ganin, a ka’idance dama kamata yayi ace Malamai su dinga fadin gaskiya ko wacce iri yayin da suke kan munbarin karatu/khudba domin gaskiya ta kowa ce, ala basshi idan hali ya basu dama wataran sun rabauta da ganin shugaban da suka aikawa da sakon a baya ta kan munabari to sai ku ji tsoron Allah su karasa aikin su na fadin gaskiya gaba-da-gaba kamar yadda ake wiya dalibai.
A gayawa Duk wani Shugaba dake ci ko Yan kanzagin sa, Shin basu san cewa su MALAMAI sune magada Annabawa ba?
Shin dama akwai abinda addini baiyi magana Akansa ba? Ko kuma ya ware cewa ba za’ayi magana akansa ba ?
Babban aikin Malamai shine shiryadda Al’umma wajen yin dik wani abu dai-dai (politics inclusive), yadda Allah ya ke so da kuma yadda rayuwar Al’umma zata inganta a duniya, kuma idan akace Al’umma ba ana nufin Talaka ba kawai, harda Shugabanni a kowanne mataki.
Idan har Malamai ba za su gayawa Gwamnati da shugabanni inda suka gaza ba ko kuma abinda ya zama matsalar Jama’a, to waye ya fisu wanda zai gayawa shugabannin indai har abinda ake tunasar dasu gaskiya ne?
Muyi hattara Jama’a !
Kudurce jin haushin Malamai a zuci kawai kan iya hana mutum cikawa da imani domin alamune na munafunci, ballantana yinkurin hana Malamai isar da sakon ayi dai-dai wanda aiki ne da Allah ya daura musu saboda sune masu shiryarwa tun da dai a yanzu babu Annabawa.
Gujewa Malamai ko korarsu daga Munbarin wa’azantarwa ko shakka babu aikine irin na Ashararai wadan da suka sanya duniya a gaba, kuma irin wadan nan mutane da yan kanzaginsu da ace a lokacin Annabawa suka zo wallahi irin sune zaka ga suna futo na futo da Annabawan ko ma su kore su daga gari.
Yana daga cikin alamun rashin rabo da tabewa, ka ga mutum ya futo karara yana fada da gaskiya ko kuma yana kare karya da kuma jin haushin duk abinda Malamai ke fada na gaskiya.
Ko wanne musulmi wakilin Allah ne a bayan kasa, kuma rayuwa bata wanzuwa sai kowannen mu ya amsa tare da isar da wakilcin dake kansa da hanyar fadin gaskiya da aiki da ita, domin Allah ne da kansa ya umarci masu Imani dasu kawarda mummunan abu da hannayen su, ko da bakunan su (wa’azi) ko kuma su kyamaci abin a zuciyoyinsu wanda shine mafi raunin Imani.
Babu shakka, halin da Al’ummar Nigeria ke ciki a yanzu na kuncin rayuwa da rashin tsaro wanda ya haifar mana da zullumi da furgici a birane da kauyuka, A yanzu ne ya kamata kowannen mu ya tashi wajen yin abinda zai iya. Ma’ana Shugabanni nayi, Malamai nayi talakawa ma nayi.
Hakika abin takaici ne matuka ace a irin wannan lokaci da kusan kowanne Dannajeriya, masu karfi da raunana, wadanda ke cikin rigar mulki da wadan da ake shugabanta ke cikin rashin tabbaci saboda ba wanda ya tsira, Amma ace wai a samu wasu daga cikin jama’a suna fushi da yadda Malamai ke gayawa gwamnati gaskiya a munbarin su harma ta kai ga dakatar da wasu ko korarsu da sauya su da wanda zaiyi akasin abinda wanda aka kora yayi.
Shin waima tsakanin fushin Allah dana shugaba idan har ba akan dai-dai yake ba, wanne ne abin tsoro? Kowanne Mai imani ya amsawa kansa.
Wannan na a matsayin irin gudummawar da zan iya bayarwa a matsayina na Dan-kasa da kundun mulkin Nigeria ya sahalewa tofa albarkacin bakinsa kuma banyi wannan rubutu da nufin gusgunawa kowa da kowanne bangare ba sai domin fatan ganin Kasa ta (Nigeria) ta samu zaman lafiya da bunkasar arziki ga kowanne Dan-kasa.
Allah ya fudda Kasa ta daga halin da take ciki a yanzu na rashin tsaro da furgici a dukkanin garuruwan Arewacin Nigeria dama sauran sassa na kasar nan dama duniya baki daya. Barka da Azumi !
Cmrd, Salisu Ismail Kabuga
Dan-jarida daga Kano
08052529040
4th, April, 2022/3rd, Ramadan, 1443 AH