Malaman Makaranta a Jihata na Karɓan Albashin N11,000 ko ƙasa da Haka  – Gwamna Zulum

 

Gwamnan Borno ya tabbatar da cewa wasu malaman makaranta a jiharsa na karɓan albashin N11,000 ko ƙasa da haka duk wata.

Farfesa Babagana Zulum, yayin martani kan wasu rahotanni, ya bayyana dalilai da yasa haka ta faru da matakin da ya ɗauka.

Wasu Hotuna da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda wasu Malamai ke karɓan albashi ƙasa da N11,000 a Borno.

Borno – Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya tabbatar da cewa akwai wasu Malamai na matakin kananan hukumomi, LEA da ke karɓan albashin N11,000 duk wata ko ƙasa da haka.

A wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na Twitter, Zulum ya ce baki ɗaya Malaman Sakandire da ke faɗin jihar na karɓan Albashi dai-dai da ƙunshin mafi karancin albashi N30,000.

Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, ne ya yi wannan bayanin yayin da yake martani kan wasu Hotunan da ke yawo a kafafen sada zumunta, waɗan da ke nuna sakon Albashin wasu Malamai ƙasa da N10,000.

Gusau ya tunatar da cewa Zulum, yayin sabunta hukumar ba da ilimin bai ɗaya ta jihar Borno, ƙarƙashin sabon shugaba, Farfesa Bulama Kagu, ranar 26 ga Oktoba, 2021, ya ce:

“Abun takaici ne har yau akwai malaman da ke karɓan albashi tsakanin N13,000-N11,000 ko kasa da haka. Duba da yanayin matsin tattalin arziki wajibi ne kowane Malami ya rika samun mafi karancin Albashi N30,000.”

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa ta aiwatar da mafi karancin Albashi kan ma’aikatan da ke matakin jiha, wanda ya haɗa da Malamai, sai dai a cewarsa hakan zai yuwu ne kan malman LEA idan an tsaftace tsarin kamar na jiha.

Kakakin gwamnan ya ce domin shirya malaman, Zulum ya kafa kwamitin da zai gudanar da gwajin cancanta ga Malamai 17,229 da ke faɗin kananan hukumomi 27 a jihar Borno.

Kwamitin ya gano cewa daga cikin waɗan nan Malaman, mutum 11,790 ba su cancanta su koyar ba, yayin da 2,389 ba su da shaidar karatu ko na Sakandire. Haka nan kuma Malamai 3,815 ba su da horon koyarwa.

A cewar rahoton kwamitin, Malamai 5,439 daga cikin 17,229 watau ƙaso 31.6% ne kacal suke da kwarewar koyarwa a makarantu.

Wane mataki Zulum ya ɗauka?

Duba da wannan rahoton a cewar Malam Gusau, gwamna Zulum na da zaɓin korar Malamai 11,790 da ba su cancanta ba kana ya yi amfani da kuɗaɗen da ake biyansu wajen aiwatar da mafi karancin Albashi ga sauran Malaman.

Sai dai Zulum ya sanar da cewa ba zai kori ko Malami ɗaya ba domin gudun ƙara yawan marasa aikin yi a jihar. Maimakon haka gwamnatin Borno zata zakulo waɗan da za’a iya ba horo yayin da sauran kuma zata canza musu wurin aiki.

Malamai 5,439 na karɓan mafi karancin Albashi

Malam Gusau ya ƙara da cewa bayan rahoton kwamitin, Zulum ya ba da umarnin fara aiwatar da mafi karancin Albashi kan malaman da suka cancanta, gabanin yanke hukunci kan sauran.

A cewarsa, ba da jimawa ba kwamishinan Ilimi, Injiniya Wakilbe, ya jagoranci taro da ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin masarautu, inda suka amince da aiwatar da umarnin gwamna kan Malaman da suka cancanta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here