Malaman Addinin Musulunci Sun Koka da Mulkin Buhari
Malaman addinin musulunci sun caccaki gwamnatin Buhari a kan rashin tsaro.
A cewarsu, ya gaza kuma duk shugabannin Najeriya su ji tsoron Allah don zai tambayesu.
Sun kuma caccaki malaman da suka yi shiru a kan lamarin, da cewa watarana zai zo kansu.
Malaman addinin musulunci sun hassala da mulkin Shugaba Muhammadu Buhari sakamakon yadda harkokin tsaro kullum suke kara tabarbarewa a Najeriya, musamman yankin arewa.
Malamai da dama sun caccaki gwamnatin Shugaba Buhari, wanda har suke nuna cewa sun dawo daga rakiyarsa.
Sun bayyana ra’ayoyinsu ne a tattaunawar da BBC tayi da su, inda suke nuna yadda Allah zai yi fushi da gwamnatin Shugaba Buhari matsawar bai shawo kan matsalar tsaro ba.
Wannan ya biyo bayan kisan manoman jihar Borno guda 43 da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka aiwatar.
BBC ta tattauna da fitaccen Malamin nan na jihar Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa, wanda ya nuna cewa wajibi ne Shugaba Buhari ya kawo karshen wannan matsalar da ta addabi arewacin Najeriya.
Read Also:
Kamar yadda yace, “Muna kira ga shugabanninmu da su san cewa Allah zai tambayesu a kan yadda suka tafiyar da mulkinsu, su kuma ji tsoron Allah, don suna da alhakin kula da rayuka miliyan 200.”
“Su tuna da alkawuran da suka dauka, na dagewa wurin kawo karshen rashin tsaro, gyara a bangaren noma da kuma hana cin hanci da rashawa,” a cewarsa.
Yace “Wadannan abubuwa su ne suka taru suka addabi Najeriya, don haka ya kamata shugaba Buhari ya shawo kansu.”
Bayan an tattauna da Malam Halliru Maraya, ya bayyanar da yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya gaza da mulkin Najeriya.
Ya ce gwamnati ta kasa aiwatar da ayyuka yadda ya kamata.Da kuma kula da rayuka da dukiyoyin al’umma, yanzu haka komai ya kazanta.
Da aka tattauna da Malam Musa Yusuf, wanda ake kira Asadus-Sunnah, ya caccaki malaman da suka zura ido suna kallon yadda harkokin tsaro suka tabarbare a Najeriya kuma suka yi shiru.
A cewarsa, “Duk malamin da yayi hudubar ranar Juma’a ba tare da ya sanya maganar tabarbarewar tsaro ba, ya ci amanar addinin musulunci.”
Ya ce bai dace a ce ana kashe musulman Najeriya ba, kuma mutum ya tattauna a kan wani maudu’in daban ba. Ya ce lallai ya kamata malamai su bude baki su yi magana, idan ba haka ba, watarana zai zo kansu.