Kwalejin Fasahar Aikin Noma: Malamai 2 da ɗalibi 1 Sun Tsero Daga Hannun ‘Yan Bindiga a Jahar Zamfara

 

Malamai biyu da kuma wani ɗalibi ɗaya da aka sace a kwalejin fasahar aikin noma dake Bakura sun tsero.

Mataimakin shugaban makarantar, Ali Atiku, shine ya bayyana haka yayin fira da manema labarai yau Litinin.

Yace hukumar makaranta ta gano cewa maharan sun yi awon gaba da ɗalibai 15 da kuma malamai guda uku.

Zamfara – Malamai biyu da ɗalibi ɗaya daga cikin waɗanda aka sace a kwalejin noma dake Bakura, jahar Zamfara sun tsero daga hannun yan bindiga, kamar yadda punch ta ruwaito.

Mataimakin shugaban kwalejin, Ali Atiku, shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin.

Atiku Yace: “Biyu daga cikin malamai da kuma ɗalibi ɗaya sun tsero daga hannun yan bindiga bayan sun sace su, sun komo makaranta da safiyar Litinin.

“Zuwa yanzun da nake magana da ku mun gano cewa maharan sun sace ɗalibai 15 duk maza, sai kuma malamai mata uku da namiji ɗaya, kuma sun kashe jami’an tsaron mu guda biyu.”

Me hukumar yan sanda tace game da lamarin? Har zuwa yanzun da muke kawo muku wannan rahoton hukumar yan sanda reshen jahar Zamfara ba tace uffan ba game da lamarin.

A baya, yan bindiga sun taba sace shugaban kwalejin aikin noma dake Bakura, Alhaji Habibu Mainasara.

Sai dai daga baya ɓarayin da suka yi garkuwa da shi sun sako shi bayan an biyasu kuɗin fansa, kamar yadda premium times ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here