Malaman mu za su Fuskanci Wahala Wajen Komawa Jami’o’insu Saboda Basu da Kudin Mota – Shugaban ASUU

 

Shugaban kungiyar malaman Jami’o’i ta Najeriya, Farfesa Emmanuel Osodoke, ya ce mambobin kungiyar za su fuskanci wahala wajen komawa jami’o’insu a ranar Litinin saboda basu da kudin mota.

Shugaban na ASUU ya bayyana haka ne a jiya Lahadi, yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels dangane da janye yajin aikin na ASUU a ckin wani shiri mai suna Sunday Politics.

Farfesa Osodoke ya ce a lokutan baya malaman Jami’a na zama a gidajen da aka tanada musu kusa da makaranta, amma a yanzu ba haka lamarin yake ba domin suna zaune ne nesa da Jami’oin da suke koyarwa saboda yawancinsu basa samar musu wuraren zama.

“A can baya, malami zai iya taka wa da kafa yaje makaranta saboda suna zaune a cikin gidaje da aka tanada musu, amma a yanzu lamarin ya sauya, inda suke tafiyan kilomitoci 20 zuwa 30 kafin isa makaranta. Ta ya ya za su iya biyan kudin mota zuwa aiki,” in ji Osodoke.

Ya ce za su fuskanci wahalhalu wajen biyan kudin motar komawa aiki domin koyar da dalibai saboda ba a biya su ba har na tsawon wata takwas.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here