Adadin Malaman Jami’a da Suka Mutu Saboda Rashin Biyan su Albashi – ASUU

 

Ƙungiyar malaman jami’a ta Najeriya ta ce ƴanƴanta 84 suka mutu saboda matsin rayuwa da suka shiga bayan an riƙe masu albashi daga watan Mayu zuwa Ogustan 2024.

“Saboda matsanancin halin da mambobinmu suka shiga daga watan Mayu zuwa Ogustan 2024 ya sa 84 daga cikin su sun mutu.

“Duk da matsalolin da ake ciki, ace ana riƙewa mutane albashin wata uku da sunan ‘ba aiki ba biyan albashi’. Mutane na faɗi-tashin yadda za su rayu amma kuna ƙara farashin mai da na lantarki, yanzu gashi nan komai ya yi tsada”

Farfesa Osodeke ya yi kiran ware ƙarin kudi domin gudanarwar jam’oin Najeriya, musamman wajen ƙarfafa gwiwar malaman jami’a.

A shekarar 2022 malaman jami’a suka shiga yajin aikin watanni takwas domin neman gwamnati ta cika alƙawurran da ta yi masu, na inganta walwala da gudanarwar jami’oi, lamarin da ya sa gwamnati ta aiwatar da tsarin babu aiki babu albashi a kan su.

A watan Oktoban 2023 shugaba Bola Tinubu ya amince da biyan su kuɗaɗen nasu na wata takwas, amma kuma malaman jami’ar sun yi ƙorafin cewa albashin wata huɗu kacal aka biya su daga cikin wanda suke bi.

Farfesa Osodeke ya ce ƙungiyar tana nan kan bakar ta cewa dole sai an biyan malaman dukkan albashin da suke bi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here