Dubban Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Guguwar sauya sheka ta kado inda dubban yan kasuwa a Sokoto suka fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP mai mulki a jihar.

Masu sauya shekar sun zargi shugabannin tsohuwar jam’iyyarsu da yin watsi da su da kuma rashin kula da jin dadinsu.

Sun kuma zargi gwamnatin tarayya da kin cika alkawaran da ta daukar masu a lokacin da gobara ta lakume shagunansu a babbar kasuwar Sokoto a farkon shekarar nan.

Sokoto – Dubban mambobin kungiyar matasan ‘yan kasuwa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Sokoto sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Hakan na zuwa ne bayan sauya sheka da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar suka yi zuwa PDP mai mulki a jihar a kwanaki.

Yan kasuwar wadanda suka yi watsi da kasancewa yan APC a cibiyar tarihi ta jihar Sokoto sun bayyana kyakkyawar shugabanci da budaddiyar manufar Gwamna Aminu Tambuwal ga dukkanin al’ummar jihar a matsayin hujjarsu, jaridar Leadership ta rahoto.

Sun kuma bayyana son kai da watsi da jin dadinsu da tsoffin shugabanninsu suka yi a matsayin dalilinsu na sauya sheka, jaridar Punch ta rahoto.

Daya daga cikin wadanda suka yi tsokaci a taron, Shuaibu Yellow, ya yi zargin cewa har yanzu ba a cika alkawarin da tawagar gwamnatin tarayya da suka ziyarci jihar lokacin da gobara ta lakume wani bangare na kasuwar Sokoto suka daukar masu ba a farkon shekarar nan.

Yellow ya ce:

“Rashin cika wannan alkawari na daya daga cikin manyan dalilan da suka sanya mu barin jam’iyyar. Dukkaninmu da muka taru a nan yan kasuwa ne kuma tun bayan gobarar, rayuwa ta yiwa yawancinmu wahala.

“Baya ga wasunmu da suka cika shagunansu da kayayyakin da aka bamu a kan bashi sannan har yanzu muke gwagwarmayar biyan bashin, wasun mu na rayuwa ne hannu baka kwarya.”

Hakazalika, Abubakar Kalambaina ya ce:

“A matsayinmu na matasa, mun yanke shawarar samawa kanmu sabuwar inuwa saboda shugabancin da muke da su, sun ci amanar yardar da muka basu.

“Sun yi watsi da jin dadinmu don saboda son zuciyarsu. Su kan je ga shugabannin tsohuwar jam’iyyarmu sannan su dawo mana da labarai yayin da wasu daga cikin mambobinmu suka rasa tudun dafawa.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here