Manchester City ta Doke Nottingham Forest

 

Manchester City ta ci wasa na shida a jere da fara Premier League ta bana, bayan da ta ci Nottingham Forest 2-0 a wasan mako na shida a Etihad.

Minti bakwai da fara wasa Phil Foden ya ci wa City kwallo, sai da ‘yan wasan City 46 suka taba kwallon kafin ta fada raga karon farko a bajintar a Premier tun bayan 2006/07.

Tarihin da yake kasa shi ne wanda Tottenham ta yi bani-in-baka sau 48 a cikin watan Agustan 2014 da ta doke Queens Park Rangers da Nacer Chadli ya ci kwallon

Minti bakwai tsakanin kwallon da City ta ci Erling Haaland ya ƙara na biyu, haka suka je hutun rabin lokaci.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne da shiga fili aka bai wa Rodri jan kati, a karawar da Anthony Taylor ya yi alkalanci.

A dakika 27 aka kori dan wasan City, inda karon farko da aka bai wa dan wasa jan kati a karamin lokaci da komawa zagaye na biyu a Premier League tun bayan 2006-07.

City ta yi kan-kan-kan a cin wasa shida da fara Premier League karo na biyu kenan, bayan bajintar da ta yi a 2016.

Ta kuma lashe wasa 20 a gida a 2023 da zura kwallo 65 kawo yanzu, wadda ta ci gaba da zama a matakin farko mai maki 18.

Karon farko da Forest ta kasa sa kwallo a raga, wadda ta yi wasa 12 a jere tana cin kwallo.

City za ta buga League Cup nan gaba, inda za ta je gidan Newcastle United daga nan ta je Wolverhampton a Premier.

Daga nan ƙungiyar Etihad za ta ziyarci RB Leipzig a Champions League da kuma zuwa Emirates domin fuskantar Arsenal a babbar gasar tamaula ta Ingila.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com