Jami’ar Abuja: Farfesa Manko ta Maye Gurbin Farfesa Aisha Maikudi

 

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sauke Farfesa Aisha Maikudi daga muƙaminta na shugabancin Jamai’ar Yakubu Gawon da ke Abuja da aka fi sani da Jami’ar Abuja.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Alhamis, ya ce shugaba Tinubu ya maye gurbinta da Farfesa Lar Patricia Manko da za ta riƙe muƙamin a matsayin riƙo na wata shida.

To sai dai sanarwar ta ce sabuwar shugabar riƙon ba za ta iya neman muƙamin idan lokacin neman matsayin ya zo ba.

A watan Yunin shekarar da ta gabata ne dai aka naɗa Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin shugabar jami’ar bayan cikar wa’adin mulkin shugaban jami’ar na shida, Farfesa Abdulrasheed Na’Allah.

Naɗin nata ya haifar da ce-ce-ku-ce a jami’ar, inda wasu ke cewa ba ta cancanta da matsayin ba.

Haka kuma shugaba Tinubu ya naɗa Sanata Lanre Tejuoso, a matsayin sabon shugaban gudanarwar jami’ar, wato Pro Chancellor.

Sanarwar ta kuma ce shugaban ƙasar ya sauke shugaban Jamai’ar Nsukka, Farfesa Polycarp Emeka Chigbu, inda ya maye gurbinsa da Farfesa Oguejiofu T. Ujam a matsayin shugaban riƙo na tsawon wata shida.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here