Martanin Atiku Kan Jawabin Tinubu a Abeokuta

 

Alhaji Atiku Abubakar, ya tuhumci Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasan All Progressives Congress (APC) da munafurci, sai yanzu yake zagin shugaba Muhammadu Buhari.

Atiku ya bayyana hakan ne a tsokacinsa game da jawabin da Tinubu yayi a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun ranar Laraba.

Tinubu, a jawabinsa ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Buhari ta taso da lamarin sauya fasalin Naira da tsadar mai saboda mutane su wahala kuma su ki zabensa a zaben 2023.

Tinubu ya shaidawa taron jama’a cewa:

“Ba sa son wannan zaben ya faru. Suna son su durkusar da shi. Za ku bar su?

“Sun fara zuwa da wani uzurin babu man fetur. Kada ku damu, idan ma babu mai, za mu taka don kada kuri’unmu.

“Idan kun ga dama, ku kara kudin farashin man, ku boye man ko kuma ku sauya launin Naira, za mu ci zaben nan.”

Jawabin Atiku

Martani kan hakan, Atiku ya fitar da jawabi ta hannun hadiminsa, Phrank Shaibu, rahoton DailyTrust.

Atiku yace:

“Saboda fusata ya kasa hana sabon tsarin daina yawon Naira da kuma sauya fasalin Naira da bankin CBN da akayi don dakile sayen kuri’u da inganta zaben wata mai zuwa, dan takaran shugaban kasa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya fara kuka.”

“Duk da cewa dukkan jam’iyyun siyasa 18 wannan doka ta CBN ya shafa, Tinubu ne kadai ya gigice. Hakazalika ya fusata shugaba Muhammadu Buhari bai son zuwa kamfensa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here