Martanin Dino Melaye da Shehu Sani Kan Kama Bishop Kukah

 

Sunan Limamin cocin Katolika na Sokoto, Mathew Kukah ya hau kanen labarai a yan kwanakin nan bayan ya zargi Shugaba Buhari da son kai.

Dino Melaye, tsohon sanata, ya yi martani a kan kiran da wata kungiya tayi na neman a kama malamin.

Dan siyasan ya bayyana dalilin da ya sa ba zai kyautu ayi amfani da yan sanda a kan malamin ba Dino Melaye, tsohon sanata, ya gargadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yunkurin kama limamin Katolika na Sokoto, Mathew Kukah, kan sukar gwamnati mai ci.

Wasu kungiyoyi a kasar sun caccaki limamin kan zargin Shugaba Buhari da son kai.

Kungiyar matasan Tiv sun zargi limamin da kira ga tunkudar da shugaban kasar sannan suka bukaci hukumomin tsaro su binciki malamin.

Sai dai, Melaye ya bayyana cewa daukar irin wannan matakin a kan shugaban addinin zai haddasa tsangwama daga mutane.

Ya yi gargadin cewa idan aka kama Kukah, za a nuna wa Shugaban kasar cewa mutane ne ke da gwamnati ba shi ba.

Ya wallafa a shafinsa:

“Kama ko kayi kokarin tozarta Bishop Kukah mu kuma za mu nuna maka cewa ba kaine ke da gwamnati ba face mutane.Suna son tsoratar da kowa. Ba zai yiwu ba. Kashe tsoro sannan ka fada wa masu mulki gaskiya.”

A Bangare Guda Sanata Shehu Sani ya yi wa kungiyar matasan arewa martani kan neman a kama Bishop Mathew Kukah.

Tsohon dan majalisar mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya shawarci matasan su mayar da hankali wurin yakar ‘yan bindiga su kyale Kukah a Sokoto.

Limamin cocin na Katolika na Sokoto ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da son kai da bangaranci wadda matasan suka ce hakan na iya raba kan kasa.

Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya, ya bukaci matasan Arewa su dena sukar Limamin cocin darikar Katolika na Sokoto, Mathew Kukah, a maimakon hakan su mayar da hankali wurin yakar ‘yan bindiga da suka addabi yankin.

A sakonsa na Kirsimeti, Kukah ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da nuna son kai. Kukah ya ce Buhari ya sadaukar da burin da Najeriya ke niyyar cimma saboda son kai da fifita yankin Arewa a kan saura.

A martaninsu, Hadakar kungiyoyin Arewa, CNG, sun zargi Kukah da kokarin lalata hadin kan kasa ta hanyar tayar da tashin hankali a tsakanin al’umma.

Kazalika, Kungiyar Matasa ta Tuntubar Arewa, AYCF, ta yi kira ayi gaggawar kama Bishop Kukah tare da bincikarsa. Kungiyar ta bayyana kalaman na Kukah a matsayin kira ga sojoji suyi juyin mulki da yi wa gwamnatin demokradiyya bore.

A sakon martanin da ya yi wa matasan na Arewa, Shehu Sani ya ce, “Ya ku matasan Arewa; Ku kyalle Kukah a Sokoto ku yi yaki da ‘yan bindigan da ke cikin wandunan ku”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here