Kare Kai Daga ‘Yan Bindiga: Martanin Gwamnan Jigawa ga TY Danjuma
Jihar Jigawa – Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya yi watsi da kiran da ake yi wa ‘yan Najeriya da su kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.
Ya bayyana cewa Najeriya ba ta kai irin wannan matsayi da za a bukaci mutane su dauki doka a hannunsu da sunan kare rayukansu ba.
A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television, Gwamna Namadi ya bayyana cewa kiran da ake yi na kare kai na iya haifar da rudani da tabarbarewar doka da bude kofar fitina.
Wannan martanin na Gwamna Namadi ya biyo bayan kalaman da tsohon Ministan tsaro, Theophilus Danjuma na cewa jama’a a Binuwai da Filato da su kare kansu daga ‘yan ta’adda.
Martanin gwamnan Jigawa ga TY Danjuma
Vanguard News ta ruwaito gwamnan Jigawa ya ce kiran zai kara dagula al’amura, inda ya ce akwai hanyoyi da dama da gwamnati ke amfani da su domin shawo kan matsalar tsaro.
Gwamnan ya ce:
Read Also:
“Shi (Danjuma) mutum ne mai fahimta sosai kan harkar tsaro, amma ni a ra’ayina, idan ka bar mutane su kare kansu, za a fada cikin rudani. Gwamnati tana iyakar kokarinta wajen samar da tsaro da tsarin tsare lafiyar al’umma.”
Gwamnan Jigawa ya ba shawara kan tsaro
Gwamna Umar Namadi ya ba da misali da yadda ya magance rikicin manoma da makiyaya a jihar Jigawa, ya ce da ya amince mutane su kare kansu, da rikicin ya fi kamari.
Ya ce:
“Kamar yadda na fada, abin da muka yi a Jigawa, da mun bar mutane su kare kansu, hakan zai janyo babbar matsala tsakanin manoma da makiyaya.
Amma lokacin da muka hau mulki, mun aiwatar da hanyoyi da dama ciki har da tattaunawa, da kuma shiga tsakani tare da sarkin gargajiya da masu ruwa da tsaki daga bangarorin biyu.”
Gwamnan ya kara da cewa bayan shawarwari da bangarorin da abin ya shafa, an kafa kwamiti domin daidaita al’amura da warware matsalolin da ke haifar da rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar.