Martanin Ƴan Najeriya Kan Batun Sayen Motocin Alfarma na Remi Tinubu
‘Yan Najeriya na ci gaba da nuna bacin rai da kwakwazo har a shafukan sada zumunta kan yunƙurin gwamnati na sayen sabbin motocin alfarma ga Uwargidan shugaban ƙasar, Remi Tinubu.
Suna kafa hujja da cewa halin da ƙasar ke ciki na ƙuncin rayuwa da matsin tattalin arziƙi, bai dace da kashe dukiyar al’umma wajen sayen motocin alfarma ga iyalin shugaban ƙasar ba.
A ranar Litinin ne, gwamnatin Najeriya ta amince da gabatar da wani ƙudurin kasafin kuɗi na cikon gibi da ya zarce naira tirliyan 2.17 ga majalisar dokokin Najeriya.
A cikin kudurin kasafin kuɗin, gwamnatin tarayya na da niyyar kashe naira biliyan 28 domin al’amuran gudanar da fadar shugaban kasa, inda za ta kashe sama da biliyan biyu wajen sayen motocin alfarma.
Ƴan Najeriya dai na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu musamman a shafukn sada zumunta, inda wasu da dama ke yin kakkausar suka a kan kashe makudan kudaden da suke gani ba zama lallai ba.
Mafi yawa dai na ganin cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba ta tausaya wa halin da talakawan kasar ke ciki, matukar za ta kashe wadannan maƙudan kuɗaɗe a lokacin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da yunwa da kuma bakin talauci.
Wannan batu ya yi daidai da ra’ayin wani mai suna Ibrahim a shafin X, wanda a baya aka fi sani da suna Tuwita.
Shi ma wani mai amfani da shafin na X Abdul-Aziz Na’ibi Abubakar ya yi gugar zana a kan batun sayen motocin alfarmar ga Remi Tinubu.
Ya dai wallafa wasu kalamai da ya yi ikirarin cewa Uwargidan shugaban ƙasar ce ta furta su a farkon hawansu mulkin Najeriya. Ga bayanin kamar haka:
“Ba a zabe mu don mu yi sata ba. Allah ya albarkaci rayuwar mijina. Ba ma bukatar dukiyar Najeriya don samun abin rayuwa. An zabe mu ne don kawo sauyi Najeriya.”
Shi kuwa @Maximus ya nuna cewa abin ya daure masa kai.
Read Also:
“Na kasa yarda da hakan saboda me ya sa za su kasance marasa tausayi irin wannan ga bukatun al’umma?
“Ina fatan a ce wannan labari ba gaskiya ba ne.”
Sai dai, yayin da akasari ke suka a kan wannan shiri na gwamnatin Tinubu, akwai waɗanda ke ganin kashe wadannan kuɗi a kan abubuwan da aka ayyana musamman motoci, abu ne mai muhimmanci wajen tafiyar da harkokin gwamnati.
Wani mai suna Kosi a shafin X ya ce idan aka yi la’akari da cewa mai yiwuwa motocin da ke ƙasa a yanzu sun tsufa, kuma suna buƙatar a sauya su.
“Abu ne da ya zama tilas ga tafiyar da harkokin mulki cikin inganci, tsoffin motocin da ake da su yanzu ba sa cikin nagarta.”
Shi kuwa Sunday Ezechukwu yana ganin cewa fadar shugaban ƙasa, ake yi wa hidima da waɗannan kudade, ba shugban ƙasa ba, saboda haka idan ana son al’amuran gwamnati su tafi yadda ya kamata, sai an tabbatar da samar da duk abubuwan da ofishin ke bukata.
A cewarsa: “Ofishin shugaban kasa daban yake da Tinubu a matsayinsa na mutum. Dole ne sai an wadata ofishin shugaban Najeriya yadda ya kamata, idan ana so ya yi nasara wajen tafiyar da mulkin kasa.”
Ko a makonnin da suka gabata, an yi ta sukar lamirin Bola Tinubu, bayan ɗansa Seyi Tinubu ya yi amfani da ɗaya daga cikin jiragen shugaban ƙasa, inda aka kai shi jihar Kano, domin kallon gasar Polo.
A baya ma, an soki gwamnatin da Tinubu ya gada a kan mulkin Najeriya, lokacin da wata ‘yar shugaban kasar na wancan lokaci ta hau jirgin shugaban kasa zuwa daukar hoton sukuwar dawaki da aka shirya mata a jihar Bauchi.
Mai yiwuwa, tayar da jijiyoyin wuyan da ‘yan Najeriya ke yi game da kashe makudan kudade wajen sayen motocin alfarma ga uwargida Remi Tinubu, ya sanya ‘yan majalisar kasar yin duban tsanaki ga dacewa ko rashin dacewar yin hakan, kafin su amince da kudurin kasafin kudi na cike gibi.
‘Yan majalisar dai su ma, sun yi ta kokarin kare matakin saya musu motocin alfarma na kimanin naira miliyan 130 kowannensu, bayan ‘yan Najeriya sun yi musu ca, tare da caccakar su a kan haka.