Martanin da Wike ya Maida wa Shugaban Jam’iyyar PDP
Gwamna Wike na jihar Ribas ya maida zazafan martani ga shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Dr. Iyorchia Ayu.
Gwamnan ya gargaɗi Ayu da cewa butulci da girman kai ba zai kai shi ko ina ba, idan shi mutun ne ya cika alƙawarin da ya ɗauka.
Wannan na zuwa ne bayan shugaban PDO Na ƙasa ya ayyana masu kiran ya sauka daga mukaminsa da yara.
Rivers – Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya caccaki shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, bisa nuna, “Butulci,” da “Girman kai” bayan an masa alfarma ya ɗare kujerar shugaban jam’iyya.
Read Also:
Channels tv ta ruwaito cewa Wike ya yi wannan furucin ne a wurin ƙaddamar da hanyoyin Omereli, yankin ƙaramar hukumar Ikwerre a jihar Ribas, ranar Alhamis.
Gwamnan ya ƙalubalanci Ayu ya nuna shi mutum ne Dattijo kuma mai gaskiya ta hanyar cika alƙawarin da ya ɗauka na sauka daga kujerar da yake kai idan har ɗan takarar shugaban kasa a PDP ya fito daga arewa.
Ya ƙara da cewa Biliyan N14bn da jam’iyya ta tara lokacin siyar da Fom na zaɓukan fidda ‘yan takara a watan Mayu, wajibi a yi adalci wajen amfani da su.
Kalaman Gwamnan sune na baya-bayan nan a kiraye-kirayen da ake ga Ayu kan ya sauka daga kujerar shugaban PDP bayan Atiku Abubakar (Daga jihar Adamawa) ya lashe tikitin takarar shugaban kasa a watan Mayu.
Ku saurari karin bayani…