Martanin ‘Yan Sanda ga Matashin da ya Turawa Matar Aure Sakon Soyaya
Wani matashi ya yi wa ‘yan sanda magana a Twitter kan yadda ya turawa matar aure sakon yana son ta amma mijinta ya je ya lakada masa duka.
Sai dai martanin da ‘yan sandan suka bada ya birge jama’a inda suka ce yayi laifi, sai dai dama mijin matar ya mika musu matashin, sai su yi masa abinda doka ta tanada.
Har ila yau, ‘yan sandan sun bukaci matashin da ya kai kansa ofishin ‘yan sanda mafi kusa, wanda hakan yasa yayi saurin goge wallafar da yayi a Twitter.
Wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Talata, 19 ga watan Yuli, ya bukaci taimakon ‘yan sanda bayan wasu sun yi masa mugun duka don ya tura wa matar aure cewa yana son ta.
A wallafarsa ta Twitter wacce yanzu aka goge, mutumin mai suna Sushant Dutt yayi ikirarin cewa wani mutum ya lakada masa bakin duka bayan yace yana son matarsa.
Read Also:
Sushant ya kara da bayyana cewa, bayan lamarin ya faru, sai ya fara tsoron halin da zai iya shiga a gaba kuma hakan yasa ya roki ‘yan sandan Punjab da su ceci rayuwarsa.
“Ranka shi dade, na tura wa wata cewa ina son ta amma mijinta ya iske ni kuma ya lakada min duka a daren jiya, ina ta bada hakuri. Amma yanzu ina tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo. Ku taimake ni, ku ceci rayuwata, ta yuwu yau ma su sake kawo min farmakin,” ya rubuta.
‘Yan sanda Punjab sun ga rokon inda suka yi masa martani da wuri.
“Bamu san me kake tsammani ba da ka yi wa matar haramtaccen sakon, amma bai dace su dake ka ba,” ‘yan sandan suka ce.
“Da sun kawo mana rahoto kuma mu yi maka abinda ya dace a karkashin tanadin doka. Dukkan laifukan nan zamu magancesu kamar yadda doka ta tanada,” suka cigaba da cewa.
A wata wallafar da ‘yan sandan Punjab din suka yi, sun bukaci Sushant da ya kai kansa ofishin ‘yan sanda mafi kusa kuma ya mika korafinsa.
Tuni dai wallafar ta janyo jinjina da tsokaci masu yawa daga jama’a wadanda suka garzaya sashin tsokaci domin fadin ra’ayinsu, India Today ta ruwaito.
Wasu sun jinjinawa ‘yan sandan kan martaninsu yayin da wasu suka yabawa mijin matar wanda suka ce yayi daidai a hukuncin da ya dauka.