Maryam Sanda: Kotun Daukaka Kara ta Tabbatar da Hukuncin Kisa

 

Kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin da alkalin wata babbar kotu da ke Abuja ya yanke wa Maryam Sanda.

A watan Janairun wannan shekarar ne alkali Halilu ya yanke wa Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Ya yi hakan ne bayan kama ta da yayi da laifin kisan mijinta mai suna Bilyami Muhammed Bello.

Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke wa Maryam Sanda a kan kisan mijinta Bilyaminu Mohammed Bello da ta yi. Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Sanda da wasu mutum uku a kan laifuka uku da suka hada da kisan kai.

Alkali Yusuf Halliru ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 27 ga watan Janairun 2020, jaridar The Cable ta bayyana.

Ta girbe abinda ta shuka, saboda an ce a kashe wanda ya kashe kuma duk wanda yayi kisa bai cancanci rayuwa ba,” Halilu yace.

“Wacce aka kama da laifin ta cancanci kisa, a don haka na yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya har sai ta mutu.”

Fusata da kuma rashin amincewa da Sanda tayi da wannan hukuncin ne yasa ta garzaya kotun daukaka kara domin bukatar sabon hukunci.

A bukatar da ta mika kotun daukaka karar ta hannun tawagar lauyoyinta, sun kwatanta hakan da tsabar rashin adalci.

Ta bayyana cewa alkalin ya dogara ne da wasu irin shaidu wadanda basu hada da “tabbaci daga bakin wacce lamarin ya faru da ita, rashin makamin kisan, rashin shaida daga a kalla shaidu biyu da kuma rashin bayanin likita a kan musabbabin mutuwar.”

Ta kara da bayyana cewa, alkalin ya yi kuskure inda ya dauka aikin dan sanda mai bincike kamar yadda ya bayyana a shafi na 76 na hukuncinsa.

Amma kuma, a ranar Juma’a, 4 ga watan Disamban 2020, kotun daukaka karar ta jaddada hukuncin kisan a kan Maryam Sanda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here