Masana Sun Aiko da Sakamakon Farko Kan Bincike a Kogon Kare Kukanka Dake Yemen
Wata tawagar masana da ta shiga Kogon nan da ake kira ‘Jahannama’ da ke Oman sun aiko da sakamakon farko tun bayan shiga kogon.
Kogon na a ƙarƙashin hamada ne a gabashin Yemen.
Read Also:
Ramin – wanda aka yi imanin yana da zurfin fiye da mita ɗari, ya kasance wani dadadden wuri da jama’a suka shafe tsawon lokaci suna guje masa.
Tsawon ƙarnuka ana ta samun labarain cewa nan ne ake ‘daure manyan rauhanan duniya”.
Masanan sun aiko da samfuran ƙasa, da wani nau’in ruwa wanda za a fara bincike a kansa.
Kazalika sun ci karo da macizai, da kwaɗi, da tumujin ƙwari da matattun dabbobi.
Wani abu da basu yi tozali da shi ba dai shine rauhanan da ake cewa an daure a ciki.