Bani da Masaniya Kan Cewa Atiku na da Ra’ayin Takara a 2023 – Gwamna Nyesom Wike
Gwamna Nyesom Wike na jahar Ribas ya bayyana cewa bai da kowani mugun nufi a kan tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Kwanan nan Atiku ya ziyarci Wike a Fatakwal, wani ci gaban da ya haifar da rade-radin cewa gwamna ya amince da tsohon mataimakin shugaban kasar.
Sai dai kuma, da yake martani kan rade-radin, Wike ya ce bai da masaniya kan cewa Atiku na da ra’ayin takara a 2023.
Read Also:
Fatakwal, Ribas – Biyo bayan hasashen cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya fara shirin zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike, ya mayar da martani.
Jaridar PM News ta rahoto cewa Wike a ranar Juma’a, 13 ga watan Agusta, ya ce ba ya da masaniyar cewa tsohon mataimakin Shugaban kasar yana son tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Legit.ng ta tattaro cewa ya yi wannan ikirarin yayin da yake magana a matsayin bako a shirin Talabijin na AIT, Focus Nigeria, a Fatakwal.
Gwamnan ya ce ba shi da masaniya game da matakin Atiku saboda har yanzu PDP ba ta raba kujerar shugaban kasa ba.