Gwamna Masari ya Koka da Rashin Tsaro da Jaharsa Ke Fama da Shi
Gwamna Masari ya karbi bakuncin babban hafsan sojojin kasa.
Faruk Yahaya ya kai ziyara Katsina don ganawa da hafsoshin sa.
Masari yace ba ya jin dadin mulkin jahar saboda annobar rashin tsaro.
Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari yace kananan hukumomi 10 cikin 34 na jahar na fuskantar munanan hare-hare kulli yaumin daga wajen yan bindiga.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin babban hafson soji, Lt Janar Faruk Yahaya, a ranar Alhamis, rahoton DN.
Read Also:
Ya bayyanawa Faruk Yahya cewa yan bindiga na sace mutane, suna jikkata wasu, suna kona gidaje, su yiwa mata fyade kuma su kora Shanu.
A cewarsa, gwamnatin jahar ba ta jin dadin halin rashin tsaron da jahar ke fama kuma saboda haka wajibi ne a kawo karshen hakan.
Yace:
“A nan jahar Katsina, mun samar da matakai uku na tsaro, daga unguwa-unguwa, zuwa kananan hukumomi, zuwa jaha, domin samar da zama lafiya.”
“Muna son zaman lafiya ya dawo da wuri kuma Sojoji su koma bariki domin yan sanda su cigaba da aikinsu.”
Gwamnan ya tabbatarwa shugaban Soji cewa gwamnatinsa za ta baiwa hukumar Sojoji dukkan goyon bayan da take bukata.