Gwamna Ganduje ya Ja Kunnen ‘Yan Kungiyar IPOB

 

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya yi kira ga masu son ɓallewa daga kasa su canza tunaninsu.

Ganduje yace hanyar da suka ɗakko ba mai bulle wa bace domin warware matsalar dake damun su Yace duniya zata daina ganin mutuncin nahiyar Africa matukar Najeriya ta kasu

FCT Abuja:- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano, yace kokarin ballewa daga ƙasa ba shine hanyar warware ƙalubalen da muke fama da shi ba.

Ganduje ya faɗi haka ne a wurin wata Lakca da jam’iyyar APC ta shirya a Abuja, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Najeriya na fama da masu fafutukar ballewa daga cikinta daga kungiyar masu son kafa kasar Biyafara (IPOB) da kuma ta yarbawa “Jamhuriyar Odudua.’

Wane Abu Ganduje yake ganin ya fi?

Gwamnan yace ya kamata masu fafutukar ɓallewa su canza tunaninsu su runguma zaman sulhu tare da watsar da tunaninsu na farko. Dailytrust ta ruwaito Gwamna Ganduje yana cewa:

“Zan sake maimaitawa Najeriya ƙasa ɗaya ce kuma ba zata rabu ba. Kundin tsarin mulkin mu ya kula da haka, bana kallon kokarin ɓallewa a matsayin hanyar warware matsalolin da suka addabi kasar mu.”

“Maimakon hanyar da suka ɗakko ina ba su shawara su canza tunaninsu, su rungumi zaman sulhu domin ta nan ne kaɗai za’a warware musu matsalarsu.”

“Bayan haka, akwai majalisar tarayya, inda za’a iya warware duk wata matsala makamanciyar wannan. Amma tattaunawa ita ce hanya mafi sauki da za’a samu dai-daituwa tsakanin gwamnati da yan ƙasa.”

Bamu son sake faɗawa yaki Ganduje ya kara da cewa babu wanda zai so Najeriya ta sake faɗawa yakin basasa, domin kasashen da suka ɓalle har yanzun rikici yaki ci yaki cinyewa.

Ganduje yace:

“Zamu so yakin basasa a Najeriya? babu wanda zai so hakan ta faru saboda haka Najeriya zata cigaba da kasancewa ƙasa ɗaya.”

“Ku duba Ethopia, Sudan da suka raba kansu har yanzun suna cikin rigingimu. Ku duba halin da Kudancin Sudan take ciki a yanzun.”

Gwamna Ganduje yace da zaran Najeriya ta rabe kasashen duniya zasu daina girmama Africa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here