Cutar Mashaƙo ta Sake Dawowa a Zagaye na Biyu a Najeriya – Hukumar Lafiya ta Duniya
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce cutar mashaƙo ta sake dawowa a zagaye na biyu a Najeriya.
Ta ce an samu ƙaruwar mutanen da ke kamuwa da cutar, da ma waɗanda ke mutuwa sanadinta, inda aka tabbatar da samun mutum 4,717 da mashaƙo ta kama.
Wani rahoto da hukumar lafiyar ta fitar, ya nuna cewa tsakanin 30 ga watan Yuni zuwa 31 ga watan Agusta, Najeriya ta ci gaba da fuskantar ƙaruwar yawan masu kamuwa da cutar.
Rahoton ya ce tun farkon ɓullar mashaƙo a shekara ta 2022, mutum 8,353 da aka yi zargin sun kamu da cutar, inda gwaji ya tabbatar da ita a jikin mutum 4,717.
Yayin da aka sallami mutum 1,857, bayan gwaji ya tabbatar, ba sa ɗauke da wata alama ta cutar, sai kuma mutum 1,048 da har yanzu sakamakon gwajinsu bai fito ba.
WHO ta kuma a cikin mutum 4,717 da suka kamu da cutar, 3,466, yara ne ‘yan shekara 14 zuwa ƙasa.
Dangane da jinsin masu fama da cutar, rahoton ya nuna cewa fiye da rabin waɗanda suka kamu da mashaƙo, mata ne.
Mutum 1,074, cikin waɗanda suka kamu da cutar ne kawai, aka yi wa cikakken riga-kafin mashaƙo, yayin da mutum 299 ba su samu riga-kafi yadda ya kamata ba.
Haka zalika, fiye da rabin wadanda suka kamu da cutar (mutum 2, 801), ba a taɓa yi musu riga-kafin mashaƙo ba, kamar yadda rahoto ya nuna.
Kuma hukumar lafiya ta duniya ta ce an samu ƙaruwar mutanen da ke mutuwa sanadin mashaƙo, kamar yadda rahoton WHO ya bayyana.
Sannan ‘yan Najeriya na cikin ƙarin hatsarin kamuwa da mashaƙo.
“Akwai ƙaruwar hatsarin kamuwa da cutar, yayin da ake samun ƙarin yankuna da ƙananan hukumomi da cutar ta ɓulla”
“A yanzu, an samu rahoton ɓullar cutar a ƙananan hukumomi 27, yayin da cutar ta fi ƙamari a ƙananan hukumomi 15 a cikin mako ukun da ya wuce”, in ji rahoton WHO.
Ministan lafiya na Najeriya, Farfesa Muhammad Pate ya kafa wani kamitin ɗaukin gaggawa a kan cutar mashaƙo, da nufin daƙile ta a ƙasar.
An samu mashaƙo a cikin jihohin Najeriya 14, yayin da Kano ta kasance inda cutar ta fi ƙamari.
Sauran jihohin da cutar take, akwai Lagos da Osun da Abuja da Nasarawa da Kaduna da Katsina da Yobe da Bauchi da Gombe da Borno da Filato da Zamfara da kuma Jigawa.
Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga ministan lafiyan ƙasar ya fitar, ta ce kwamitin zai gudanar da ayyukansa cikin gaggawa domin daƙile yaɗuwar cutar mashaƙo zuwa sauran jihohin Najeriya, da kuma bai wa mutane taimako.
Read Also:
Kwamitin dai na ƙarƙashin jagorancin babban daraktan hukumar bunƙasa ayyukan kula da lafiya a matakin farko (NPHCDA), Dakta Faisal Shu’aib da daraktan hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta ƙasar (NCDC ), Dr. Ifedayo Adetifa.
Ya kuma ƙunshi wakilai daga ma’aikatar lafiyar ƙasar da wakilan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, da na UNICEF da wakilan kwamitin sarakunan arewacin Najeriya kan tabbatar da lafiya a matakin farko
Farfesa Pate ya ce hukumar lafiyar ƙasar za ta shirya babban gangami domin wayar da kan jama’a game da cutar mashaƙo.
“A nan ne sarakuna za su ba da gudunmawa. Dole ne a wayar da kai game da cutar, da irin hatsarin da ke tattare da ita, da matakan da ya kamata, mutane su ɗauka don kauce wa cutar mashaƙo”, in ji Farfesa Pate.
Ya ƙara da cewa dole ne mu ɗauki matakin gaggawa a daidai lokacin da yaranmu ke koma wa makaranta.
Mece ce cutar mashaƙo?
Dakta Usman Bashir, likitan kula da lafiyar al’umma ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano, ya ce cutar mashako dai wata cuta ce da ke kama yara waɗanda suka kai shekara biyar da kuma manya da suka haura shekara 60.
Dr Usman ya ce cutar tana an fi samunta a wuraren da ba a fiya yin alluran rigakafi ba. Kama garkuwar jikin ɗan adam take kamawa ta yi mata mummunar illa.
Likitan ya ce cutar tana saurin kisa saboda ba a gane ta da wuri idan an kamu, kuma a mafi yawan lokuta sai ta kai ga yaro ya fara numfashi cikin wahala, ko kumaya gaza cin abinci ko ya kamu da zazzabi mai tsanani ko kuma yawan tari.
Ya ce cutar na yaɗuwa ne ta hanyar zama cikin cunkoso a ɗaki ɗaya, musamman wanda aka rufe tagoginsa babu wajen shan iska da kuma waɗanda ba a yi wa allurar rigakafi ba wadda ke bayar da garkuwa ga kwayoyin halittar ɗan adam da ke yaƙar kwayoyin cutar.
Ya kuma ce tana ɗaya daga cikin cutukan yara da ke saurin kisa, sannan tafi tashi a lokacin sanyi.
Yadda cutar ke kama mutum
Tsohon shugaban hukumar yaki da cutuka masu yaɗuwa ta Najeriyar Farfesa Abdussalam Nasidi, ya shaida wa BBC cewa cutar mashaƙo, na kama maƙogoro ne, tare da hana mutum sakat.
Ya ce: ”Idan ta kama mutum za ta riƙe masa wuya kamar an shaƙe ka, idan ta kama yaro idan ba Allah ne ya kiyaye ba a gaban iyayensa za a rasa shi, don haka babbar barazana ce”.
Wasu alamomin cutar
Alamomin cutar na fara bayyana a jiki ne cikin kwanaki biyu zuwa biyar.
Tari
Zazzabi mai zafi
Rashin cin abinci
Kumburin cikin baki
Numfashi sama-sama
Yoyon hanci
Gajiya
Hanyoyin kauce wa kamuwa da cutar mashaƙo
Likitoci sun ce hanya ɗaya ta kauce wa kamuwa da cutar mashaƙo ga manya da ƙananan yara ita ce yin allura, saboda za ta kashe ƙwayoyin cutar da ke jikin mutum.
Yana da muhimmanci a wayar da kan al’umma wajen yi wa yara allurar riga-kafi, domin hakan zai iya magance ba wai mashaƙo kaɗai ba har da cutar sarƙewar haƙora da ƙyanda da sauransu.