Cutar Mashaƙo ta Kashe Mutane 600 a Najeriya
Sama da mutum 600, waɗanda yawancinsu yara ne suka rasa rayukansu a Najeriya sanadiyyar cutar diphtheria tun bayan ɓullar ta a watan Disamban 2022.
Hukumomi sun ce jimillar mutum 14,000 ne suka kamu da cutar, wanda hakan ya zarta mutanen da suka kamu da ita a lokacin da ta ɓarke a 2011, inda mutum 98 suka kamu.
Read Also:
Kano, wadda ke a arewacin Najeriya, ita ce jihar da ta fi fama da matsalar, inda aka samu mutum 500 da suka mutu sanadiyyar cutar, sai dai hukumomi sun ce lamarin na lafawa a yanzu.
Diphtheria cuta ce ta mashaƙo wadda ke saurin yaɗuwa, kuma tana shafar sassan jiki irin su hanci da maƙoshi.
Haka nan cutar kan haifar da gyambo a ciki ko kuma ta shafi fatar jiki.
Cutar na yaɗuwa ne ta hanyar tari da atishawa daga masu fama da ita.
Duk da cewa ana iya samun kariya daga cutar ta hanyar rigakafi, yawancin yaran da suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar ba su samu rigakafin ba.