APC Zuwa PDP: Masoyin ɗan Siyasa ya Salwanta Rayuwarsa Gurin Murnar Sauya Shekar Uban Gidansa a Abuja

Wani masoyi ɗan gani kasheni na shugaban karamar hukuma a Abuja ya rasa rayuwarsa sanadiyyar hatsarin mota.

Mutumin ya rasu ne yayin da suke tsaka murnar sauya shekar Uban Gidansa Ciyaman na Gwagwalada daga APC zuwa PDP.

Sauran mutum uku da suke cikin motar suna kwance a Asibiti, Mamacin kuma an masa jana’iza yadda musulunci ya koyar.

Abuja – Wani magoyin baya kuma ɗan a mutun shugababan ƙaramar hukumar Gwagwalada a a babban birnin tarayya Abuja, ya rasa rayuwarsa a hatsarin Mota.

Daily Trust ta rahoto cewa mutumin mai suna Awwal Idris, ya rasu ne yana tsaka da murnanr sauya shekar Uban gidansa Ciyaman, Alhaji Adamu Mustapha, daga APC zuwa PDP.

Rahoto ya tabbatar da cewa ragowar mutum uku dake tare da Mamacin a cikin Motar, yanzu haka suna kwance a wani Asibitin kuɗi dake Gwagwalada, Abuja.

Lamarin ya auku ranar Asabar da misalin ƙarfe 11:00 lokacin da tawagar Ciyaman din ke kan hanyar zuwa gundumar Dobi, inda zai tabbatar da sauya sheƙarsa a hukumance ta hannun shugaban PDP na Dobi, Abubakar Sarki.

Yadda mutumin ya rasa rayuwarsa a hatsarin

Bayanan da muka samu sun nuna mana cewa Motar da suke ciki ta sauka daga kan titi kuma ta wuntsila sannan ta dira a cikin hanyar ruwa dake bakin titin.

Bisa haka ne, Idris ya rasa rayuwar nan take a inda hatsarin ya auku, sauran kuma aka garzaya da su Asibitin domin kula da lafiyarsu.

Shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Gwagwalada, Alhaji Yunusa Abdullahi, ya tabbatar da faruwar hatsarin ga manema labarai ta wayar Salula.

Ya ce Mamacin, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Leda, inda Ciyaman na Gwagwalada ya fito, an masa jana’iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here