Zaku San Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta’addanci a Lokacin da ya Dace – EFCC ga ‘Yan Najeriya
Shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati wato EFCC Abdulrasheed Bawa, ya ce ‘yan Najeriya za su san sunayen masu daukar nauyin ta’addanci a lokacin da ya dace.
Read Also:
Yana magana ne yayin wani shirin siyasa na tashar talabijin ta Channels jiya Alhamis.
Bawa, wanda ya fadi lokacin da yake jawabi a fadar shugaban kasar a jiyan, ya ce likitoci sun shaida masa cewa bashi da wata matsala, don haka a yanzu ya murmure.
”Makoshi na ne ya dan bushe, sai likitoci suka bukaci in sha ruwa sosai, daga baya kuma na wartsake ba wata matsala yanzu” inji shi.