Gwamnatin Tarayya ta Bayyana Cewa ana Samun Mata Masu Juna Biyu 830 Dake Mutuwa Wurin Haihuwa Kullum a Najeriya

 

FG tace mata masu juna biyu aƙalla 830 suke mutuwa a duk rana ta sanadiyyar wani abu da ya danganci juna biyu ko wajen haihuwa.

Ministan lafiya na ƙasa, Dr. Osagie Ehanire, shine ya bayyana haka a wani taron ƙarawa juna sani da aka shirya kan binciken lafiyar mata masu juna biyu.

Yace ya zama wajibi Najeriya ta miƙe tsaye wajen yin aiki tuƙuru ta kare lafiyar mata da ƙananan yara.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ana samun mata masu juna biyu 830 dake mutuwa wurin haihuwa kullum a Najeriya, jimulla 302,950 a shekara, kamar yadda thisday live ta ruwaito.

Wanna ƙiddigar na cikin jawabin ministan lafiya na ƙasa, Dr. Osagie Ehanire, a wajen taron ƙarawa juna sani da kuma bada shawarwari a a kan bincike da aka gudanar na lafiyar mata masu juna biyu da ƙananan yara a yankin Africa.

Ohanire, wanda daraktan lafiya da ƙididdiga a ma’aikatar lafiya, Dr. Ngozi Anazodo, ta wakilta, yace: “Najeriya da take da kashi ɗaya cikin ɗari na yawan al’ummar duniya, amma ita keda 13% na mace-macen mata masu juna biyu da jarirai yan ƙasa da shekara biyar a duniya.”

“A kowace rana a Najeriya ana samun mata 830 dake mutuwa ta sanadiyyar wasu cututtuka dake da alaƙa da juna biyu ko wajen haihuwa.”

“A duk mace ɗaya data mutu wajen haihuwa, to za’a samu wasu da dama da suka ji mummunan rauni ko wasu cututtuka a wajen haihuwan.”

Ministan ya ƙara da cewa gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakan da ya kamata shine zai rage yawan waɗannan mace-macen wurin haihuwa a ƙasar.

Yace aikin ƙara wayar da kan mata su fahimci muhimmancin zuwa duba lafiyar su zai sa a ɗauki dogon lokaci kafin rage yawan mutuwar mata da ƙananan yara a Najeriya.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ƙara azama wajen inganta lafiyar ƙananan yara da jarirai, hakanne kaɗai cigaban da aka samu zuwa yanzun.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here