Yadda Matar Aure ta Kashe ɗan Kishiyarta a Jihar Kano
Kano – An cafke wata matar aure bisa zargin zuba guba a abincin ɗan kishiyarta ɗan kimanin shekara ɗaya tal a jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa matar ta gurfana a gaban kotun majistire mai zama a Nomansland a ƙaramar hukumar Fagge bisa tuhume-tuhumen da suka shafi kisa.
Kano: Yadda matar ta kashe yaron kishiya
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, matar da ake zargin ta zuba maganin kashe ƙwarin da aka fi sani da fiya-fiya a abincin ɗan ƙaramin yaron.
Hakan ya zama sanadin mutuwar jaririn da bai wuce shekara ɗaya da haihuwa ba, wanda ba a kai ma ga yaye shi ba.
Read Also:
Lauyan masu shigar da kara, Barista Abdussalam Dan Maidaki Sale shi ne ya gabatar da tuhume-tuhumen da ake wa matar wanda suka ta’allaka kan kisan kai.
Ya shaidawa kotun cewa laifin da ake zargin matar ta aikata ya saɓa wa tanadin sashi na 221 da ke ƙunshe a kundin dokoki Fenal Kod.
Wane mataki kotu ta ɗauka?
Sai dai kotun majistire ta bayyana cewa ba ta da hurumin sauraron wannan shari’a bisa tanadin dokokn kotunan majistire.
Bisa wannan dalili ne alƙalin kotun mai shari’a Hajara Safiya Hamza ta ɗage zaman zuwa ranar 30 ga watan Oktoba, 2024.
Amma gabanin haka ta bayar da umarnin a iza ƙeyar matar da ake zargin zuwa gidan gyaran hali kafin zuwan wannan rana.