Mataimakin Gwamnan Kano ya yi Murabus Daga Mukaminsa

 

Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam ya yi murabus daga mukaminsa a yau Juma’a, 27 ga watan Maris, 2026.

Kwankwasiyya ta bayyana cewa Aminu Gwarzo ya yi murabus ne bisa kishin kasa, da son wanzar da zaman lafiya a Kano.

Gwarzo ya yi martani ga yunkurin da majalisar dokokin jihar ta fara na tsige shi, yana mai cewa bai aikata laifin komai ba.

Kano – Cikin wani babban sauyi na siyasa a jihar Kano, mataimakin Gwamna Kwamared Aminu Abdussalam ya yi murabus daga muƙaminsa a yau Juma’a, 27 ga Maris, 2026.

Kakakin tafiyar Kwankwasiyya, Dr. Habibu Sale Mohammed, ne ya sanar da hakan ta hanyar wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.

Mataimakin gwamnan Kano ya yi murabus Wannan murabus yana zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta ƙaddamar da tsarin tsige shi daga kan mulki, in ji rahoton Daily Trust.

Ko da yake Kwamared Aminu Gwarzo ya shigar da ƙara a babbar kotun tarayya dake Kano domin dakatar da shirin majalisar, kotun ta yi watsi da buƙatarsa, matakin da ya ƙara matsa masa lamba har ya kai ga sauka daga kan kujerarsa.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwarzo ya ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da kuma ba gwamnati damar gudanar da ayyukanta ba tare da tangarɗa ba.

Wani dalili na murabus din Aminu Gwarzo

Sanarwar Dr. Habibu Sale ta ce:

“Yanayin da ake ciki a yanzu ya kawo cikas ga gudanar da ayyukan ofishin Mataimakin Gwamna yadda ya kamata, shi ya sa ya zama dole a bar ofishin domin ya ci gaba da amfanar al’umma.”

Dr. Habibu ya jaddada cewa wannan murabus ba yana nufin Kwamared Aminu ya amince da zarge-zargen da majalisar dokoki ke masa ba ne.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

“Mataimakin gwamnan ya jaddada cewa ba shi da laifi, kuma tarihin aikinsa shaida ne kan gaskiya da riƙon amana da yake da su ga mutanen jihar Kano.”

Shirye-shiryen babban zaɓen 2027 Bayan barin ofishinsa, sanarwar ta nuna cewa Abdussalam zai mayar da hankali sosai wajen ƙarfafa tafiyar Kwankwasiyya domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen sheƙa da rarraba kawuna a tsakanin manyan jiga-jigan siyasar jihar.

A ƙarshe, jagororin tafiyar sun yi kira ga magoya bayansu da su kwantar da hankulansu su zauna lafiya, tare da bin doka da oda.

Wannan murabus dai ya bar tambayoyi da dama a zukatan Kanawa game da wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf zai naɗa a matsayin sabon mataimakinsa domin kammala ragowar wa’adin mulkinsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here