Ondo ta Tsige Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jahar
Rikicin siyasa a majalisar dokokin jihar Ondo ya yi sanadiyar tsige mataimakin kakakin majalisa, Iroju Ogundeji.
An cire Ogundeji daga matsayin a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, a yayin zaman majalisar.
A nan take kuma majalisar ta zabi Samuel Aderoboye a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar.
An tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Iroju Ogundeji, a yayin zaman majalisa na yau Talata, 24 ga watan Nuwamba.
Read Also:
Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsige Ogundeji ya biyo bayan rikicin siyasa da ya addabi majalisar jihar ta kudu maso yamma.
Legit.ng ta tattaro cewa mambobin majalisar dokokin sun kuma zabi Samuel Aderoboye daga mazabar Odigbo a nan take domin maye gurbin mataimakin kakakin majalisar.
A tuna cewa shugaban majalisar ya dakatar da Ogundeji a baya tare da wani dan majalisa, Adewale Williams.
Dukkanin yan majalisar biyu sun kasance daga cikin yan majalisa tara da suka yi adawa da yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Agboola Ajayi.
Ajayi wanda ya bar PDP zuwa jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) ya kara da gwamna mai ci, Rotimi Akeredolu wajen neman kujerar gwamnan jihar.