Matakan da Miyetti Allah ta Dauka Wajen Rage Rikicin Manoma da Makiyaya
Jihar Kwara – Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association (MACBAN), ta bayyana matakin da ta dauka wajen rage rikicin manoma da makiyaya.
Kungiyar MACBAN ta haramtawa yara masu karancin shekaru kiwon dare a fadin jihar Kwara a yunkurin rage rigingimu tsakanin manoman da masu kiwo.
Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban MACBAN na kasa, Alhaji Baba Othman Ngelzarma ne ya bayyana haka yayin kaddamar da shugabancin kungiyar na jihar Kwara.
Sauran matakan da Miyetti Allah ta dauka
Read Also:
Kungiyar MACBAN ta dauki matakin haramta kiwon dare a fadin jihar Kwara domin rage matsalolin da ke jawo rigingimu tsakaninsu da manoma.
Shugaban kungiyar, Alhajai Ngelzarma ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa kiwon dare wata hanya ce ta takalar tsokana da neman rigima da gangan.
Dalilin daukar matakan da Miyetti Allah ta yi
Kungiyar makakiyan kasar ta ce ta dauki matakan haramta kiwon dare da barin kananan yara su rika kiwo saboda magance rikicin manoma da makiyaya.
Kungiyar ta bayyana cewa dangantaka mai kyau tsakanin manoma da makiyaya abu ne mai muhimmancin gaske, inda ta bukaci shugabannin kungiyar su tabbata an bi dokokin.