Gwamnatin Legas Tayi wa Matan ‘Yan Sanda da Aka Kashe Goma ta Arziki

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwoolu, a ranar Alhamis ya bada milyan goma ga kowanne cikin matan jami’an yan sanda shida da aka kashe yayin zanga-zangan EndSARS.

Gwamnan ya yi hakan ne domin cika alkawarin da yayi lokacin ganawarsa da yan sandan jihar.

“Wasu daga cikin jaruman yan sandanmu sun rasa rayukansu yayin karemu lokacin zanga-zangan EndSARS,” gwamnan yace yayin gabatar da kudaden garesu.

“Wadannan hafsoshi ne da aka tura kare iyalanmu daga yan baranda amma aka kashesu a rikicin.

A yau ina farin cikin sanar da rabon milyan goma-goma ga kowanne cikin iyalan wadannan yan sanda.”

“Gwamnatin jiha za ta dauki nauyin karatun yaransu har su kammala jami’a.”

Jami’an yan sandan da aka kashe sune ASP Yaro Edward, Sifeto Ayodeji Erinfolami; Sifeto Aderigbigbe Adegbenro; Sifeto Ehibor Samson, Sajen Bejide Abioudun da Sifeto Igoche Cornelius.

Hadimin gwamnan kan sabbin kafafen yada labarai, Jubril Gawat, ya bayyana hakan a shafin na Tuwita.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here