Abin da Matasa za su yi Bayan Kammala karatu – Ganduje 

 

Tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa., Abdullahi Ganduje, ya ce tsarin ilimin Najeriya na da nakasu.

Abdullahi Ganduje ya shawarci matasa da su fantsama wurin koyon sana’o’in dogaro da kai domin magance rashin aikin yi.

Shugaban jam’iyyar ya jaddada cewa gwamnati ba za ta iya samarwa kowa aikin yi ba, don haka dole matasa su kirkiro aikin da kansu.

Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da tsananin rashin aiki duk da da yawansu sun kammala karatu.

Kamar yadda ya ce, dalibai ba sa koyon dabarun sana’o’in dogaro da kai sakamakon nakasu da ke a tsarin karatun kasar, wanda ke haifar da rashin ayyukan yi, rahoton Vanguard ya bayyana.

“Tsarin ilimin Najeriya ya gaza” – Ganduje

Ganduje ya yi jawabin ne a taron bude shirin horarwa na sana’o’in hannu domin matasa a Legas, wanda shugaban matasa na jam’iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya shirya.

Tsohon gwamnan Kanon ya yarda cewa idan aka fara horar da matasa sana’o’i, Najeriya za ta samar da masu digirin da ba karatu kadai suka sani ba, har da kasuwanci da kirkire-kirkire.

An ce Ganduje ya samu wakilcin mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu, Cif Emma Eneukwu, kuma ya yi kira da ayi garambawul a fannin ilimi.

Ya jajanta yadda masu digiri a Najeriya suka kware a turanci amma babu aikin hannu, banda ire-irensu dake kasashen waje kama China da Indiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here