Matashi ya Bayyana Yadda Aka ki Bashi Aiki a Gini Mai Hawa 21 da ya Rufta a Legas
Wani Matashi abinda ya faru da shi ranar gini mai hawa 21 ya rufto kan mutane a unguwar jahar Legas.
Matashin ya bayyana yadda aka ki bashi aiki a wajen ranan saboda shi Musulmi ne kuma yana Sallah.
Kawo yanzu yanzu an ciro gawawwakin mutum 43 da ginn ya rufta da su yayinda wasu suka tsallake rijiya da baya.
Injinyan ya bayyana cewa ginin ya rufto kan dukkan wadanda ke ciki kimanin sa’o’i biyu bayan da ya bar wajen.
Ya ce Mai ginin ya fitittikesa ne saboda kawai shi Musulmi ne kuma ba zai iya daukan mai kiran sunan Allah a wajen aikinsa ba.
Sikiru wanda mazaunin jihar Legas ne ya bayyana hakan a hirar da yayi na AN24 Tv kwana daya bayan aukuwan lamarin.
A cewarsa:
“Na tafi intabiu ne da shugaban Foursquare Mr Femi don yin aikin Injiniya a wajen. Lokacin intabiun na yi masa bayanin irin ayyukan da nayi a baya.”
Read Also:
“Da farko sai ya tambayeni, wani Coci nike zuwa, sai nace masa ni Musulmi ne. Sai yace, ‘Sam ba zan iya aiki da Musulmi ba.’ Ban ji dadi ba, bai kamata addini ne ya shafi aikin da zan yi ko iyawa na ba.”
“Sai ya fadi da yaren Yarbanci ‘Idan kana gidana yanzu sai kace za kayi Sallah? Ko zaka rike kiran Alhamdulillah a gina?’.”
Sikiru ya bayyana cewa maimakon ko da baya son Musulmi, yayi kokarin fada masa a kaikaice cewa ba zai daukesa aiki ba, amma ya fito fili ya bayyana cewa ba zai dauki Musulmi ba.
Yace:
“Na yi masa bayanin wahalhalun da na sha a baya, nayi aiki a gona, lokacin da na gama makaranta da sauransu, sai yace kila don addini na ne yasa ban samu cigaba a rayuwa ba. Kuma a gaba kowa ya fadi hakan, leburori, birkiloli.”
Ina hanyar tafiya gida abokina ya kirani A hirar, Sikiru yace ba tare da bata lokaci ba ya bar wajen kuma ya kama hanyarsa ta tafiya gida.
Yayinda yake hanyar tafiya gida sai ya yada zango wajen abokinsa don ya wuce fushin abinda ya fuskanta.
Yace:
“Kawai sai abokina ya kira yana tambayena ina nake, yace min shin na samu labarin abinda ke faruwa game da ginin kuwa, ginin fa ya rushe.”
“Da muke duba Instablog, sai naga daidai inda muka zauna ya rushe. Abin bai min dadi ba.”