Matashi ya Kashe Budurwar da Zai Aura a Jihar Kano

 

Jihar Kano – Rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ta cafke wani matashi, Abubakar Kurna bisa zarginsa da kashe budurwar da zai aura, Naja’atu Ahmad.

Ƴan sandan sun gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun majistire mai zama a Nomansland a ƙaramar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Kotu ta bada umarnin garƙame Abubakar

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa alkalin kotun, mai shari’a Huda Haruna ya ba da umarnin a tsare Abubakar a gidan gyaran hali zuwa ranar 21 ga watan Nuwamba.

Alƙalin ya ɗauki wannan matakin ne saboda kotun ba ta hurumin sauraron shari’a mai girma irin wannan.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Logged in as Khadija Garba. Log out?

Please enter your comment!