Hankulan Jama’a Sun Tashi Bayan Matashi ya Kashe Matar Babansa

 

Ana nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar faɗa a cikin gida, al’amarin da ke kaiwa ga kisa tsakanin iyali.

Wannan na zuwa ne bayan da a jihohin Katsina da Kano aka samu wasu matasa samari sun kashe matan iyayensu ta hanyar kai musu hari saboda zargin su ne suka saka aka saki iyayensu mata.

Masana lafiyar kwakwalwa na cewa, ba sai mutum yana da matsalar kwakwalwa yake aikata mummunan laifi ba.

Lamari na baya-bayan nan ya faru ne a unguwar Rijiyar Zaki cikin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano a karshen mako.

Inda aka zargi wani matashi da caccakawa kishiyar mahaifiyarsa sukundireba, sannan kuma ya shake wata karamar yarinya abin da ya yi sanadin mutuwarsu.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ya ce tuni suka kama wanda ake zargin domin gudanar da bincike.

A watanni baya ma a jihar Katsina an samu irin wannan matsala inda ake zargin wani matashi ya kashe wasu makusantansa.

Bayanai na cewa shi dai wanda ake zargi da kashe kishiyar mahaifiyar tasa ya aikata kisan ne saboda zargin da ya yi cewa itace ta yi sanadin da aka kori mahaifiyarsa daga gidansu.

Likitoci irin su Dakta Aminu Shehu Ibrahim kwararren likitan kwakwalwa a asibitin Malam Aminu Kano ya ce akwai wani bangare na kwakwalwar mutum da ke takawa masa birki a duk lokacin da zai aikata wani abu.

Sai dai kuma idan bai kosa ba, to akwai yiwuwar a samu tunzuri na aikata abin da mutum zai yi dana sani.

Bugu-da-kari masanan na ganin watsi da iyaye maza ko mata ke yi da ‘ya’yansu tare da cuzguna musu, shi ne babban abin da ke ruruta matsalar al’amarin da ke jefa rayuwarsu cikin kunci da damuwa.

Ana danganta wannan batu da samo asali daga fitar iyayensu mata daga gidajen aurensu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here