Matashi na Tallata Kodarsa ga Mai Niyyar Siya Don Biyawa Kaninsa Kudin Makaranta a Kasar Kenya
Felix Joel na son tura kaninsa jami’ar Kenyatta ko ta kaka a kasar Kenya.
Ya fara tallar kodarsa ga mai niyyar siya don samun kudin biyawa kaninsa kudin makaranta.
Matashin yace ya kasance mai taimakon yan uwansa tun lokacin da mahaifinsu a 2017.
Kenya – Wani mutumi mai kimanin shekaru 26, Felix Joel ya kasance mai tallafa ma yan uwansa na tsawon shekaru har ta kai yanzu abin ya fara gagararsa.
A wani tattaunawa da Tuko.co.ke wanda Legit.ng ta shaida, matashin dan kasuwan mai zama a Kisumu’s Manyatta ya bayyana yadda ya zama mahaifi a kananan shekarunsa.
Yace, yana da kanne yanuwa uku wadanda mahaifinsa ya tafi ya barsu dashi bayan rasuwarsa a 2007.
A cewarshi,
“Ina aji daya na karamar sakandare lokacin dana fara kula dasu da wata yar kwarya kwaryar sana’a da nakeyi saboda mahaifiyata bata aiki.
Read Also:
Joel ya kara da cewa bayan ya ajiye karatunshi a gefe ne ya fara sana’a gadan gadan har ya bude shago a Migori wanda hakan yake taimaka mai wajen biyan bukatun yan uwan na shi.
A cewarsa:
“Har na samu wata kwangila ina kaiwa wata makaranta wake amma da aka ce dalibai su koma gida waccen shekarar sanadiyyar COVID-19 ban kuma kara samu ba.”
Abinda yasa Joel zai siyar da kodar shi
Dan uwan Joel, Morgan mai shekaru 17 zai fara Jami’ar Kenyatta ranar 4 ga Octoba kuma zai karanci Ilimin kimiyyar gona.
Saboda yadda abubuwa suka gagara kawai sai Joel ya yanke hukuncin zagayawa da takarda akan titi yana tallar kodarsa saboda ya samu dan uwansa ya fara makaranta.
“Ina da matsaloli da yawa da bazan iya ma lissafo su yanzu ba. Ba mata daya Mahaifina yake dashi ba, toh yanzu maganar da nake maka ma ba a gida muke zaune ba, wannan wani labarin ne daban, ” Cewar Joel.
Har zuwa hada wannan rahoton Joel bai samu wani taimako ba amma yana sa rai sakon shi zai isa ga abokin arziki.