Matashi a Titin Jahar Legas na Tallata Kodarsa

 

Wani fusataccen dan Najeriya ya bayyana a titin jahar Legas yana tallata kodarsa ga mai sha’awar siya.

A bidiyon wanda shafin Naijaloaded suka wallafa a Instagram, an ga mutumin a gefen titi dauke da takarda yana tallar.

Mutane da dama sun yi zargin tsabar talauci, kunci, takaici da matsin rayuwa ne suka janyo har mutumin ya aikata hakan

Legas – Bidiyon wani fusataccen dan Najeriya ya karade kafafen sada zumuntar zamani inda aka gan shi a tsakiyar titi yana shelar burinsa na sayar da kodarsa.

A bidiyon, an ga mutumin sanye da bakin tabarau a gefen titi dauke da takarda wacce ya rubuta “Ga koda mai kyau ta siyarwa”.

Tuni mutane suka fara cece-kuce kowa yana tofa albarkacin bakinsa inda wasu suke cewa tsabar matsin rayuwa ne ya janyo masa hakan.

Wahala, kunci, takaici da talauci sukan saka mutum yayi abinda ba a saba gani ba musamman irin na wannan mutumin mai burin sayar da sassan jikinsa.

Ga dukkan alamu mutumin bai damu da maganar mutane ba.

A bidiyon wanda Naijaloaded suka wallafa a shafinsu na Instagram an ga mutum sanye da bakaken kaya a bakin titi yana rike da wata takarda wacce yake tallata kodarsa.

Al’amarin da ya faru a jahar Legas. Legit.ng bata gano kwakkwaran dalilin da ya janyo har mutumin yayi wannan abu ba har a lokacin rubuta wannan rahoton.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here