Yadda Matashiya ta Rungumi Sana’ar POP

 

Wata kyakkyawar mace ‘yar Najeriya mai suna Okeke Stephanie ta ba da mamaki yayin da ta bayyana sana’ar da ta ke yi.

Stephanie dai ta kama sana’ar POP ne, lamarin da wasu ke ganin ba sana’a ce da ta dace diya mace ba.

Sai dai, ta bayyana irin kwarin gwiwar da take dashi, da kuma kalubalan da ta kawar kafin kai wa ga hakan.

Jihar Delta – Wata ‘yar Najeriya mai suna Okeke Stephanie, ta ba da mamaki yayin da ta bayyana irin sana’ar da take yi don samun na kashewa.

Stephenie dai ‘yar jihar Delta ce, kuma ta ce ta kama sana’ar daben saman daki na POP ne domin ta kashe kwarkwatar da ke kanta.

Ta kuma bayyana cewa, ta kan sha suka da zolaya game da wannan aikin da take yi, inda wasu ke cewa aiki ne na maza.

A cewar Stephanie, ba jama’ar gari kadai ba, har iyayenta ba su nuna farincinsu ga wannan sana’a ta yin POP ba.

Duk da haka, ta tattara hankalin wuri guda, inda ta tabbatar da ta koyi sana’ar yadda ya dace har kowa ya yarda ita kwararriya ce.

A cewarta, duk da sana’ar na sanya a ganta futu-futu, duk da hakan tana iya shiga mai kyau idan ta ji sha’awar caba kwalliya.

Matsalolin da take fuskanta

Stephenie ta koka da yadda wasu ke mata ganin wacce ta kama sana’ar da bata cancanci diya mace ba. Wasu kuwa kallo suke ba ma za ta iya yin aikin yadda ya kamata ba kasancewar ita ba namiji bace.

Duk da haka, ta ce ita fa a kan gaba take wurin aikinta, domin kuwa duk wanda ta zauna ta cancarawa aiki sai ya yaba kuma tana yin iya kokarinta.

Yabo daga jama’ar intanet

Abiolaamao ya ce:

“Najeriya tana da tarin masu basira, Ya Allah azurtamu da shugabanci na gari.”

Jasonsfoodsng ne ya ce:

“Ki tafi kawai yarinya, Allah ya albarkaci sana’arki ta hannu, ya kuma cika miki burin rayuwarki.”

Ochonojone ya rubuta:

“Ga kyau ga kuma aiki tukuru.”

Ib.flora ya ce:

“Kai, abun burgewa! ‘Yar uwa abu ya yi kyau.”

Ogesbakedtreats ya ce:

“Aiki dai aiki ne kawai, sannu da aiki ‘yar uwa.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here