Gwamna Matawalle ya Dakatar da Sarkin da ya Nada ‘Dan Bindiga a Matsayin Sarkin Fulani

 

Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya dakatar da sarkin Yandoton Birni, Aliyu Marafa saboda nada dan bindiga Adamu Aliero-Yankuzo, Sarkin Fulani.

Gwamnatin na Zamfara ta nesanta kanta da nadin sarautar da aka ce an yi ta kuma kafa kwamiti na bincike don gano dalilin da yasa sarkin na Yandoto Birni ya aikata abin da ya yi.

A halin yanzu, gwamnatin ta Zamfara ta umurci Alhaji Mahe Garba Marafa, Hakimin Ƴandoto ya cigaba da kula harkokin masarautar.

Zamfara – Gwamna Jihar Zamfara Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Birnin Ƴandoto, Aliyu Marafa saboda naɗa shugaban yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Adamu Aliero-Yankuzo, Sarkin Fulani, rahoton Daily Trust.

Matakin da masarautar ta dauka na nada ɗan bindigan sarauta ya janyo cece-kuce inda da dama suka soki naɗin sarautar da aka yi wa ɓata garin.

Amma, cikin wata sanarwa da sakataren gwamnati, Kabiru Balarabe ya fitar, gwamnatin ta nesanta kanta daga matakin sarkin, ta kuma dakatar da sarkin sannan ta kafa kwamiti don bincike kan lamarin, Daily Nigerian ta rahoto.

Ga sanarwar a kasa:

Abin da sanarwar ta kunsa

Sanarwar ga al’umma

1. Muna sanar da mutane cewa Gwamnatin Jihar Zamfara ta nesanta kanta daga nadin sarautar Sarkin Fulani da ake ce Sarkin Birnin Ƴandoto na ƙaramar hukumar Tsafe ya yi. Don haka Mai Girma Gwamna, Hon. Bello Mohammed Matawalle, MON (Shattiman Sokoto) ya umurci a dakatar da sarkin nan take.

2. Hakazalika, Mai girma gwamnan ya amince da nada kwamiti don binciken abin da yasa Sarkin ya dauki matakin. Kwamitin ta ƙunshi:

a) Hon Yahaya Chado Gora – Shugaba

b) Hon Yahaya Mohd Kanoma – Mamba

c) Hon Mohd Umar B/Magaji – Mamba

d) Hon Lawal Abubakar Zanna – Mamba

e) Isah Muhd Moriki (Sakataren dindindin mai murabus) – Mamba

f) Barista Musa Garba – Sakatare

3. A halin yanzu, an umurci Alh Mahe Garba Marafa, Hakimin Ƴandoto ya cigaba da kula da harkokin masarautar.

Sa hannu

Kabiru Balarabe Sardauna (Lamidon Kaura Namoda) Sakataren Gwamnatin Jiha.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here