Babbar Matsalar da ta Damu Arewacin Najeriya – Audu Ogbeh
ACF ta ce yaran arewa sun mayar da rikici hanyar samun nishadi.
Audu Ogbeh, shugaban ACF ya ce kullum tsaron arewa tabarbarewa yake yi.
Ya fadi hakan ne lokacin da ya kaiwa gwamna Zulum ziyara Shugaban ACF, Audu Ogbeh, ya ce harkar tsaron arewa kullum tabarbarewa take yi.
Ogbeh ya jagoranci mutane zuwa Maiduguri don jajanta wa gwamnan a kan kashe-kashen Zabarmari.
Fiye da manoma 40 ‘yan Boko Haram suka kashe a kauyen da ke karkashin karamar hukumar Jere a makonnin da suka gabata, The Cable ta wallafa.
Read Also:
Tsohon ministan ya ce babbar matsalar da ke addabar arewa shine yadda aka mayar da siyasa ta zama hanyar da kowa yake son ya samu kudi da ita.
Ya kara da cewa siyasa kuwa bata samar da cigaba a ko ina.
“Muna cikin matsananciyar damuwa. Duk wanda a cikinmu baya cikin damuwa yanzu haka, bai haifu ba. Saboda ba mu da abinda za mu bai wa yaranmu, kuma rikici ba zai kai mu ko ina ba,” kamar yadda wata takarda ta ranar Litinin ta yanko maganganun Ogbeh.
“Babbar matsalar da muke da ita shine ba mu da wata hanyar samu, in ban da siyasa. Kuma babu inda siyasa za ta kai wata al’umma.
“Dolene mu kara gina jihar Borno, mu gina arewa sannan mu gina Najeriya. Ba mu da wasu masana’antu, harkar noma ta lalace sannan yaran mu sun mayar da rikici da tashin hankali a matsayin hanyar samun nishadi,” yace