Abubuwan da ke Kawo Matsalar Tsaro a Najeriya – Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa

 

Shugaban hukumar yaki da rashawa a Najeriya ICPC ya ce gurbacewar tattalin arziki da kuma rashawa da ta’annati ne manyan abubuwan da ke ruruta matsalar tsaro a Najeriya.

Bolaji Owasanoye a jawabin da ya saki yace idan ba’a sanya ainun nazari kan alakar dake tsakanin rashawa da rashin tsaro ba, za’a samu matsala.

Shugaban na ICPC ya kara da cewa akwai bukatar hada kai da hukumar NSCDC saboda kawo gyara a Najeriya.

Abuja – Shugaba hukumar yaki da rashawa da ta’annati watau ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya ce abinda ya haddasa matsalar tsaro a kasar shine cin hanci da rashawa da kuma gurbacewar tattalin arziki.

DailyNigerian ta ruwaito cewa kakakin ICPC , Azuka Ogugua, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Laraba, 11 ga Agusta, a Abuja cewa Shugaban na ICPC ya yi wannan magana ne yayinda ya karbi bakuncin kwamandan NSCDC, Ahmed Audi.

Owasanoye ya kara da cewa hadin kan wadannan hukumomin gwamnati biyu na da muhimmanci don kawo gyara kasa da kuma samun labaran leken asiri domin yaki da rashawa.

The Guardian ta ruwaito cewa kwamandan NSCDC Audi ya bukaci taimakon ICPC wajen horar da jami’an hukumarsa kan yadda ake tattara labaran leken asiri da kuma bincike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here